Shugaban Ƙasar Sin Xi Jinping zai yi jawabi a yayin buɗe taro zagaye na biyu na yarjejeniyar COP15

Daga CMG HAUSA

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta sanar da cewa, a gobe Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai gabatar da jawabi ta kafar bidiyo, yayin bude taro zagaye na biyu, na wakilan bangarorin da suka sanya hannu kan jarjejeniya kasancewar mabambantan halittu karo na 15 ko COP15.

Sannan, Shugaban taron MDD kan wanzuwar mabanbantan halittu, kuma ministan ma’aikatar kula da muhalli da muhallin halittu ta kasar Sin Huang Runqiu, ya yi kira ga sassa masu ruwa da tsaki da su tashi tsaye, wajen jajircewa, da nuna hikima da kwazo, domin toshe gibin dake akwai, da sabani, ta yadda za a cimma nasarorin da aka sanya gaba.

Huang Runqiu ya yi tsokacin ne a jiya Talata, yayin taron manema labarai, karkashin taron sassan da suka amince da yarjejeniyar MDD game da wanzuwar mabanbantan halittu karo na 15 ko COP15 a takaice.

Huang ya kara da cewa, sakamakon rawar da daukacin sassan masu ruwa da tsaki a yarjejeniyar suka taka, taron ya cimma manyan nasarori. Cikin su har da amincewa da shawarwari guda 23, wadanda suka kai kaso daya bisa uku na jimillar shawarwarin da ake bukata wajen cimma nasarar taron. Ya ce a wasu sassa masu muhimmanci ma, dukkanin bangarorin sun yin musayar ra’ayi mai zurfi kan matsayar su da mahangar su.

An bude taron game da yarjejeniyar MDD mai nasaba da wanzuwar halittu mabanbanta ne a makon jiya, kuma taron ya shiga lokaci mafi muhimmanci, yayin da ya rage mako guda a fitar da kundin da zai yi bitar matakan sauya asara, da koma-bayan da aka samu, game da wanzuwar mabanbantan halittu.

Bisa tanadin taron, za a gudanar da zaman dandalin ministoci tsakanin ranakun 15 zuwa 17 ga watan Disambar nan, domin warware batutuwa masu sarkakiya dake cikin kundin.

Da take tsokaci yayin taron manema labaran da ya gudana, babbar sakatariyar taron Elizabeth Maruma Mrema, ta ce “Muna bukatar wannan tattaunawa, domin cimma nasarar fitar da kyakkyawan tsari mai inganci, na gudanar da ayyukan da za su dakatar da asarar da ake tafkawa, a fannin wanzuwar halittu mabanbanta, tare da share fagen farfado da fannin yadda ya kamata”.

Mai fassara: Safiyah Ma, Saminu Alhassan