An kusa kai Arewa bango – ACF

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

ACF ta bayyana hakan ne a yayin taron kwamitinta na ƙoli na 78 da ta yi a ranar Alhamis , 21 ga watan nan na Agusta, 2025 a birnin Kaduna.

Shugaban ƙungiyar Mamman Osuman shi ne ya faɗi hakan inda ya yi gargaɗin yana mai cewa yanzu ba lokaci ba ne da yankin zai zauna ya kame bakinsa ya yi shiru yana ganin irin yadda al’amura ke ta taɓarɓarewa a yankin.

Ya yi kira ga shugabannin Arewa da ‘yan yankin da su tashi tsaye su hada kai ganin yadda harkar tsaro ke ƙara lalacewa da yadda ake ci da gumin yankin da da kuma yadda matsalar muhalli ke ƙara zama barazana ga yankin gabaɗaya.

ƙungiyar ta ce yanzu ba lokaci ba ne da za ta zauna ta zura ido ko ta kawar da kanta da cewa komai yana tafiya daidai a ƙasar ba.

Osuman ya nuna takaicinsa kan irin rayukan da ake ci gaba da kashewa a kullum a arewacin Nijerriyar.

“Mun rasa yara matasa maza da mata da tsofaffi a sanadiyyar bala’o’i da ambaliya da ayyukan miyagu ɓata-gari da ‘yan ta’adda. Halin da muke ciki a yankin babban abin damuwa ne a garemu, wanda a don haka nake kira a garemu mu yi nazari tare da addu’a,” ya ce.

A tattaunawarsa da BBC mai bayar da shawara ga ƙungiyar ta ACF, Bashir Hayatu Gentile, ya ce, a lokacin taron ƙungiyar ta yi nazari tare da tsokaci kan waɗannan abubuwa da suka damu ƙungiyar na matsalolin da ke addabar yankin.

Ya ce, ”Abubuwa ne sahihai suke ganin yanzu su ne matsalolin ‘yan arewa waɗanda ake son lalle-lalle a yi kama-kama kuma a yi wa gwamnati tsinke aka lalle ta yi wani abu na magance waɗannan matsaloli.

”Ba abin da ya fi damun Arewa yanzu kamar matsalar tsaro da yadda ake sace-sace da kashe-kashen mutane a kan hakan ne ƙungiyar ta fitar da matsaya ta ganin lalle yankin ya tashi tsaye ya haɗa kai tare da ganin matsa wa gwamnati a kan ta ƙara ƙaimi wajen ganin ta magance wa Arewa waɗannan katutun matsaloli,” a cewarsa.

Gentile ya ce a jawabin da shugaban ƙungiyar ya gabatar a wajen taron na Kaduna, ya ce, ”A jawabin da ya fitar ya yi kira ga gwamnatin tarayya cewa, lalle-lalle haƙurin Arewa ya kusa ƙarewa gwamnati ta sake wasu dabaru don ganin cewa an daƙile wannan abin da ke damin Arewa.”

Mai bayar da shawarar ya ce ƙungiyar ta ACF ta damu ne ganin irin rahoton da ƙungiyar Amnesty International ta fitar wanda ya nuna cewa : ”A cikin mulkin shekara biyu da Shugaba Tinubu an kashe mutum 10217 kuma dukkaninsu a arewacin Nijeriya ne, wannan shi ne ya sa ƙungiyar ta ACF ta damu.”

Ya ce wannan bayan ɗimbin mutanen da aka sace ake kuma ci gaba da sacewa da kashewa da tashin garuruwa kusan a kullum a arewacin Nijeriyar.

”Wannan abin da ya fi damu na kwana-kwana nan a ƙaramar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina, wanda aka shiga masallaci aka samu mutane suna salla da asuba aka kashe su aka ƙona su. A rahoto da aka fitar shi ne cewa mutum 27 aka kashe amma a labarin damuke samu ma ya fi haka.

Tun da ƙungiyar Amnesty suka fitar da wannan rahoto babu wani daga cikin gwamnati da ya fito ya ƙaryata wannan rahoto shi ne ya sa ACF take ganin to lalle ya kamata a sauya tsari.

By ukarofi