An mayar wa Juventus maki 15 ɗin da aka kwashe mata a Serie A

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

An mayar da maki 15 da aka kwashe wa Juventus a Serie A, bayan da wata Kotun Sauraren Ƙararrakin wasanni ta yi umarnin a sake bibiyar laifin da ake zargin ƙungiyar.

A watan Janairun 2023 aka hukunta Juventus, bayan da aka sami ƙungiyar da laifin bayar da bayanan karya na hada-hadar ƙungiyar.

Da wannan hukuncin Juventus ta koma ta uku a teburin Serie A, amma za a iya sake hukuntata idan an sameta da laifin bayan bibiyar zargin da ake mata.

Daraktan Tottenham, Fabio Paratici bai yi nasara kan ɗaukaka ƙarar da ya shigar ba, wanda aka dakatar wata 30, kan laifin da ake zargin Juventus.

Tsohon daraktan wasannin Juventus, Paratici ɗaya ne daga daraktoci 11 daga ƙungiyar ta Italiya da aka hukunta.

Ya ajiye aikin da yake yi a Tottenham, bayan da aka faɗaɗa hukuncinsa na dakatarwa a fanni tamaula a faɗin duniya ba iya Italiya ba.

Lamarin ya faru ne a lokacin da ƙungiyar Arewacin Landan ke neman kocin da zai maye gurbin Antonio Conte, bayan da suka raba gari.

Kamar yadda aka yi watsi da ɗaukaka kakar Paratici, an kuma qi amincewa da ɗaukaka ƙarar da tsohon shugaba, Andrea Agnelli da babban jami’i, Maurizio Arrivabene da daraktan wasanni, Federico Cherubini da suka shigar.

Saura wasa takwas a ƙarƙare gasar Serie A, kenan Juventus ta mayar da AC Milan mataki na biyar, a teburi ita kuwa Roma ta koma ta huɗu a babbar gasar tamaula ta Italiya.