An sace Rabaran Mikah Suleiman a Gusau

‘Ƴan bindiga sun sace wani limamin cocin Raymond katolika, Rabarand father Mikah Suleiman.

Mai magana da yawun yan sandan jihar Zamfara shine ya tabbatar da aukuwar wannan lamarin.

“Yace Rabarand father ɗin an sace shi ne a gidan sa da misalin karfe 3 na safiyar Asabar a gidan sa dake Damba. Ya bada tabbacin tuni an tura jami’ai su fara bincike don ganin an kuɓuto shi cikin gaggawa”