An yi jana’izar Kwamishinan Ciniki da Masana’antu na Jihar Jigawa, Alhaji Salisu Zakari

Daga WAKILINMU

A ranar Asabar da ta gabata ɗaruruwan mutane daga sassa daban-daban na faɗin ƙasar nan suka halarci jana’izar Kwamishinan Ciniki da Masana’antu na Jihar Jigawa, Alhaji Salisu Zakari (Cigarin Haɗejia) a fadar Mai Martaba Sarkin Haɗejia.

Jana’izar da aka gudanar da ƙarfe 11 na safe ta samu halarta manya ‘yan siyasa da masu sarauta da sauran al’ummar garin Haɗejia.

Rasuwar marigayin ta jijjiga al’umma gani irin gudunmawar da yake bayarwa a sarautar ƙasar Haɗejia da ma cigaban Jihar Jigawa.

A shekarar da ta gabata Masarautar Haɗejia ta naɗa shi sarautar Ci-garin Haɗejia na farko biyo bayan ɗimbin nasarorin da yake kawo wa garin.

Cikin wata sanarwar da Gwamnatin Jihar Jigawa ta fitar, Gwamnan Jihar, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya bayyana wannan rashi a matsayin babban giɓi a jihar da ma ƙasa baki ɗaya.

Haka nan, ya yi amfani da wannan dama wajen miƙa ta’aziyya da ban haƙuri ga ‘yan uwa da abokan arziki dangane rashin.

Alhaji Salisu Zakari ya rasu ne a ranar Juma’a da daddare a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano biyo bayan gajeruwar rashin lafiya da ya yi fama da wanda wanda ya zama ajalinsa.