Okowa ga Tinubu: Ni da Atiku babbar barazana ce ga APC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Jihar Delta, kuma mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa a Jam’iyyar PDP, Ifeanyi Okowa, ya ce takararsu tare da Atiku Abubakar ta kasance babbar abin barazana ga APC, a zaven 2023.

Okowa na faɗin hakan ne a wani martani da ya mayarwa ɗan takarar shugabancin Nijeriya a APC, Asiwaju Bola Tinubu, wanda yake cewa mutumin da ya zaɓa domin yi masa mataimaki ya fi na Atiku.

Gwamnan dai ya ja hankalin Tinubu, yana mai cewa ya mayar da hankali wajen tattauna batutuwa masu muhimmanci ba na mutum ba, a shirye-shiryensu na yaƙin neman zaɓen 2023.

Okowa ya ce zain APC na ɗan takara da mataimakinsa Musulmi, ya buɗewa PDP ƙofar sa’a, saboda ‘yan Nijeriya za su so ganin an yi musu adalci a matsayin tarayya.

Ɗan takarar ya ce Atiku Abubakar ya zaɓe shi ne saboda ƙwarewarsa ta siyasa, da kuma irin gudunmawar da ya bayar wajen gina ƙasa da riƙe jiharsa cikin aminci a tsawon shekara bakwai na mulkinsa.