Ana zargin ‘yan bijilante da kashe malamin makarantar allo a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ana zargin ‘yan ƙungiyar sintiri (vigilante) da kashe wani malamin makarantar allo a unguwar Davai, da ke Ƙaramar Hukumar Gwale a Jihar Kano.

Shi dai Musa Mai-Almajirai, sanannen malamin Ƙur’ani ne a unguwar, inda yake da ɗaruruwan almajirai.

Ana zargin ‘yan ƙungiyar sintirin da yi wa malamin dukan tsiya a ofishinsu bayan da aka kai shi can bisa zargin da wata mata ta yi masa na yunƙurin satar yaro.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa ɗan malamin, Ibrahim ya shaida mata cewa, ”mahaifin nasa yana tafiya ne sai ya ji kukan jariri sabuwar haihuwa a wata bola.

“Sai ya je ya ɗauki yaron, sai kawai wata mata da ta hango shi, sai ta kwarma ihu tana ce masa ɓarawon jariri.

”Kururuwar da matar ta yi ce ta janyo ‘yan ƙungiyar sintirin da sauran jama’ar unguwar waɗanda suka rufe shi da duka,” inji ɗan.

Ya ƙara da cewa, ”daga nan sai suka tafi da shi ofishinsu suka ci gaba da dukansa. Daga baya ya faɗi a sume.”

Ya ce: ”Bayan da wasu ‘yan unguwar suka gane shi sai suka garzaya da shi asibiti, inda ya cika a hanya.”

Ɗan malamin ya shaida wa jaridar cewa ‘yan sanda sun kama shugaban ‘yan sintirin na unguwar, mai suna Munkaila, inda ake bincikensa a caji ofis na Rijiyar Zaki.

Ita ma rundunar ‘yan sanda a Jihar Kano, ta bakin kakakinta, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an kama mutane 6 da a ke zargin na da hannu a kisan, kamar yadda ya shaida wa Freedom Radio.