Tsohon Sufeto-Janar, Tafa Balogun ya kwanta dama

Daga BASHIR ISAH

Allah Ya yi wa tsohon Sufeto-Janar na ‘Yan Sandan Nijeriya, Mustapha Balogun, rasuwa.

Majiya daga ahalin marigayin ta tabbatar wa Daily Trust rasuwar, sai dai babu wani ƙarin bayani a kan haka.

Marigayin wanda ya zama Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda a watan Maris, 2002, ya rasu ne kwanaki huɗu kafin cikarsa shekara 75 da haihuwa.

An haifi Bologun ne a ranar 8 ga Agustan 1947 a Ila-Orangun da ke Jihar Osun.

A halin rayuwarsa, marigayin ya shahara ne a 2005 bayan da aka gurfanar da shi a kotu bisa zargin tafka mundanar sama da Dala miliyan $100 cikin shekaru ukun da ya yi a matsayin Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *