Ma’aikatar tsaron Sin ta yi bayani game da matakan soji da Ƙasar ta ɗauka

Daga CMG HAUSA

Kakakin ma’aikatar tsaron ƙasar Sin Tan Kefei, ya ce ƙasar Sin ta ɗauki matakan soji domin tsaron kai, bisa la’akari da yadda kakakin majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi ta ziyarci yankin Taiwan, a ranar 2 ga wata.

A cewarsa, wannan yunƙuri ne da ya saba da alƙawarin Amurka na kin goyon bayan ‘yancin Taiwan, kuma taƙala ce ta siyasa mai tsanani ga ƙasar Sin, yana mai cewa, kasar Sin na adawa da kin lamuntar hakan.

Rundunar yankin gabashi ta runduanr ‘yantar da al’ummar ƙasar Sin PLA, ta shirya kai farmaki na hadin gwiwar sojoji, ta ruwa da ƙasa tare da iko da yankin sararin samaniyarta, da kuma wasu atisayen soja a teku da sararin samaniya, a kewayen tsibirin Taiwan, wanda ke zaman lahani ga kawancen Amurka da Taiwan.

Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CMG Hausa