APC na ƙara samun tagomashi ƙarƙashin jagorancin Ganduje – Kamalu Baƙo Lamiɗo

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An bayyana fitaccen ɗan siyasa kuma ɗaya daga cikin dattawa a Jam’iyyar APC a jihar Kano,  Alhaji Nasiru Aliko ƙoƙi da cewa mutum ne mai son zaman lafiya da yake da kyakkyawar mu’amala tsakaninsa da  al’umma, ba kawai  ‘yan siyasa ba, da ma kowane irin mutum, shi ya sa duk wata hidima da ta taso masa ɗimbin mutane ke halarta.

Hon. Kamalu Bawo Lamiɗo ne ya bayyana hakan da yake zantawa da ‘yan jarida a yayin ɗaurin auren ɗaya daga dattawan jam’yarr APC, Alhaji Nasiru Aliko da aka yi a unguwar ƙoƙi wanda ya samu halartar masu ruwa da tsaki na jam’iyyar na ƙasa ƙarƙashin jagorancin Ganduje.

Ya ce yanzu jam’iyyar APC sai ƙara tagomashi take a jihar Kano dama ƙasa baki ɗaya, duk da halin da ake ciki amma mutane sun fahimci abu ne da ya shafi duk duniya ba kawai ƙasar nan ba, kuma suna da fatan cin zaɓe a Kano da ƙasar nan a 2027.

Kamala Baƙo Lamiɗo ya yi nuni da cewa tunda jagoransu Dakta Abdullahi Umar Ganduje  ya zama shugaban jam’iyyar APC na ƙasa sai daɗa karɓuwa jam’iyyar take yi, hakan ya sa a zaɓuka da aka yi na gwamnoni a wasu jihohi APC  ce ke yin nasara har ma inda  jam’iyyar ‘yan hamayya suke da gwamna APC ta yi nasara.

Ya ƙara da cewa wannan alama ce  da take nuna ƙwarewa da gogewa ta jagoran siyasarsu Dakta Abdullahi Umar Ganduje a siyasa, dama ya taɓa faɗa musu cewa shi siyasa ya karance ta ne ba a kan hanya ya tsinceta ba ilimi ta ne da shi.

Hon. Kamalu Baƙo Lamiɗo ya ce wannan irin nasarori da ake samu ya daɗa tabbatar musu da sanin Dakta Abdullahi Ganduje ga siyasa ya zama malaminta don haka a ci gaba da bai wa jam’iyyar APC goyon baya domin bunƙasa cigaban ƙasar nan.

By ukarofi