Attajirai kaɗai ke cin moriyar tallafin mai – Minista

Daga AISHA ASAS

Ƙaramin Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Ƙasa, Clem Agba, ya jaddada buƙatar da ke akwai na duba fannin fetur don cire tallafin man baki ɗaya.

Ministan ya faɗi haka ne saboda a cewarsa, a halin da ake ciki attajirai ne kaɗai ke amfana da tallafin amma ban da talakawa.

Agba ya yi wannan bayani ne a wajen wani taro da aka gudanar kan batun shugabanci a Abuja a Talatar da ta gabata.

Ya ce, “Wasu na ganin cewa wai idan aka cire tallafin fetur baki ɗaya talaka zai wahala, ta yaya zai wahala? Ai ba abu ne da ya shafi abinci ba.

“Manyan motocin da ake amfani da su wajen jigilar abinci zuwa sassan ƙasa ba su amfani da fetur sai man dizal wanda tuntuni an cire tallafinsa.

“Don haka masu cin moriyar tallafin fetur su ne attajiranmu.”

Ministan ya jaddada muhimmancin ƙawancen gwamnati a buɗe wanda ya bayyana da cewa hakan wata hanya ce ta bai wa ‘yan Nijeriya damar sanin mawuyacin halin da tattalin arzikin ƙasa ke ciki don samar da mafita.