01
Dec
Daga BASHIR ISAH Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa, an samu raguwar mace-mace sakamakon cutar kanjamau (AIDS) da kashi 70 a faɗin duniya tun 2004. Majalisar ta ce duk da wannan matsayi da aka cimma, har yau AIDS na kashe mutum guda a cikin duk minti guda. Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, António Guterres ne ya bayyana haka cikin saƙon da ya fitar albarkacin Ranar Yaƙi da AIDS ta Duniya ta 2023. António Guterres ya ce, "ya zama wajibi mu ga bayan AIDS a matsayin ƙalubale ga lafiyar al'ummar duniya ya zuwa 2030." Ya ƙara da cewa, domin kawar da…
