Editor

9513 Posts
Shaye-shaye: Ya dace gwamnati ta tallafa wa ƙungiyoyi – Abdulrazaq Shehu

Shaye-shaye: Ya dace gwamnati ta tallafa wa ƙungiyoyi – Abdulrazaq Shehu

Daga AMINU AMANAWA a a Sakkwato Idan da akwai wata matsala da a yanzu ta fi damun iyaye da dama, musamman a jihohin Arewa bai wuce matsalar fatauci ko tu'ammali da miyagun ƙwayoyi ba musamman a tsakanin matasa da kuma mata. Malam Abdulrazak Shehu sanannen mai fafutikar yaqi da matsalar ne musamman a jihohin Sakkwato, Kebbi da kuma Zamfara, wanda ma har ya samar da qungiya sukutum domin yaƙi da matsalar wato "Center for Sensitization Against Drug Abuse" a turance.A zantawarsa da wakilinmu na Sakkwato Aminu Amanawa ya tattauna da Malam Abdulrazak Shehu wanda ya yi bayani sosai kan matsalar…
Read More
Hajjin 2024: An buƙaci maniyyatan Sakkwato su gaggauta biyan kuɗaɗensu

Hajjin 2024: An buƙaci maniyyatan Sakkwato su gaggauta biyan kuɗaɗensu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta jihar Sakkwato (PWA) ta yi kira ga maniyyatan jihar da su gaggauta biyan kuɗin kujerunsu kafin ranar 25 ga watan Disamba da Hukumar Hajji ta Ƙasa ta tsayar. Shugaban Hukumar Alhaji Aliyu Musa ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Sakkwato jim kaɗan bayan ganawarsa da jami’in rijistar alhazan ƙananan hukumomi 23 da sauran masu ruwa da tsaki a jihar. Ya ce kiran ya zama wajibi bisa la’akari da gyare-gyare da matakan da Masarautar Saudiyya ta vullo da su gabanin aikin Hajjin 2024.…
Read More
Anas Ɗahir ya zama gwarzon musabaƙar Alƙur’ani na Filato

Anas Ɗahir ya zama gwarzon musabaƙar Alƙur’ani na Filato

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU a Jos Hafiz Anas Abubakar Ɗahir da ya wakilci Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa shi ne ya samu nasarar zama gwarzon Musabaƙar Haddar Alƙur'ani Maigirma na shekarar 2023, wanda Gidauniyar Musabaqar Alƙur'ani Maigirma ta Ƙasa Reshen Jihar Filato ta saba shiryawa duk shekara karo na 38. Ɗalibin, wanda ya fito daga Madarasatu Al-Bunyan ya samu nasara ne da maki 92.5 cikin ɗari, a rukunin haddar Alƙur'ani da Tafsir. Yayin da Hafiza Hafsat Ahmad a vangaren mata ta samu zama gwarzuwa da maki 89.3 cikin xari. Shugaban Gidauniyar Musabaƙar Alƙur'ani Mai Girma ta ƙasa Reshen Jihar Filato,…
Read More
Majalisar Wakilai ta gayyaci hukumar jami’o’i bisa soke darasin aikin lauya a Jami’ar NOUN

Majalisar Wakilai ta gayyaci hukumar jami’o’i bisa soke darasin aikin lauya a Jami’ar NOUN

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Majalisar Wakilai ta gayyaci muƙaddashin Babban Sakatare na Hukumar Jami’ar Ƙasa (NUC), Darakta Janar na Majalisar Ilimin Shari’a kan dakatar da kwas ɗin karatun shari'a a Jami’ar NOUN. Sauran waɗanda aka gayyata sun haɗa da shugabannin makarantar koyon aikin shari’a ta Nijeriya, da shugaban kwamitin Benchers da mataimakin shugaban jami’ar NOUN. Hakan ya biyo bayan wani quduri ne da aka yi tsakanin mataimakin shugaban jami’ar NOUN, Farfesa Olufemi Peters da wasu ɗaliban da suka kammala karatun shari’a da suka koka da shugaban kwamitin ilimin jami’ar, Abubakar Fulata, a Abuja ranar Alhamis. An zargi NOUN da dakatar…
Read More
CBN ga bankuna: Ku cigaba da hada-hada da dukkan takardun Naira

CBN ga bankuna: Ku cigaba da hada-hada da dukkan takardun Naira

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Babban Bankin Nijeriya ya umurci dukkanin bankuna da su cigaba da bayarwa tare da karvar duk wani nau'i na takardun kuɗin Nijeriya, tsofaffi da sababbi waɗanda aka sakewa fasali. Muƙaddashin Daraktan Sadarwa na Kamfanin Ali Hakama ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba. Hakan ya biyo bayan umarnin da Kotun Ƙolin ƙasar ta bayar a ranar Laraba 29 ga watan Nuwamba, 2023, wanda ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya ya nemi a ƙara tsawaita amfani da tsofaffin takardar kuɗin Naira. A hukuncin da kotun ta yanke, kotun ta cigaba da…
Read More
CORHSPS kundi ne mai amfani wajen ci gaban Kano – SSG Bichi

CORHSPS kundi ne mai amfani wajen ci gaban Kano – SSG Bichi

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano Majalisar Tsofafin Manyan Sakatarori da Tsofaffin Shugabanin ofishin Ma'aikatun Gwamnatin Kano 134 da suka yi ritaya a lokuta daban-daban kuma suke raye yanzu haka da ake kira Council of Retired Heads of Service and Permanent Secretaries Kano State CORHSPS-KN ƙarƙashin shugabancin Alhaji Isah Mahmoud Babban kundi ne mai amfani ga al'ummar Kano da ma Nijeriya baki ɗaya kasancewar sun yi aiki har zuwa ƙololuwar muƙami da ake kaiwa na ƙwarewa a aikin gwamnati. Don haka a cewarsa za su cigaba da tuntuɓarsu a wajen tafi da gwamnati don cigaba Kano kamar yadda dama da wasu…
Read More
Hamas da Isra’ila sun sake tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta

Hamas da Isra’ila sun sake tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta

Isra’ila da Hamas sun amince da qara tsawaita yarjejeniyar da ke tsakaninsu da aƙalla kwana guda, matakin da ke zuwa mintuna ƙalilan gabanin kawo ƙarshen makamanciyar yarjejeniyar ta kwanaki shida da aka faro. Wannan mataki dai na zuwa ne bayan tsanantar kiraye-kirayen ganin an ɗauki wannan mataki, inda sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres ke miqa buƙatar ganin an samar da yarjejeniyar dindindn tsakanin ɓangarorin biyu tare da isar da kayakin agaji cikin gaggawa a Gaza. Sai dai sanarwar ma’aikatar tsaron Isra’ila ta ce an ɗauki matakin ƙara kwana guda a yarjejeniyar ne, don samun damar sakin ƙarin…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: An naɗa sabon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa

Da Ɗumi-ɗumi: An naɗa sabon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa

Daga BASHIR ISAH 'Yan Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa sun zaɓi Danladi Jatau a matsayin sabon Kakakin da zai ci gaba da jagorancin majalisar. A ranar Juma'a aka naɗa Jatau a matsayin sabon shugaban majalisar jihar biyo bayan tsige Ibrahim Balarabe Abdullahi da Kotun Ɗaukaka Ƙara mai zamanta a Abuja ta yi daga kujerasa. Kazalika, 'yan majalisar sun naɗa Mohammed Oyanki a matsayin Mataimakin Kakakin majalisar. Jatau na wakiltar shiyyar Kokona ne a majalisar, yayin da Oyanki ke wakiltar mazaɓar Doma ta Arewa.
Read More
Na’urar VAR na ɓarna fiye da gyara – Bincike

Na’urar VAR na ɓarna fiye da gyara – Bincike

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Masu ruwa da tsaki na cigaba da miƙa ƙorafe-ƙorafe game da kuskuren da na’urar taimakawa alƙalin wasa ta VAR ke c gaba da tafkawa a wasannin gasar Firimiyar Ingila, ta yadda na'urar ke sahale bugun fenariti a wajen da bai kamata ba, baya ga soke ƙwallayen da suka cancanta. Lamarin da ya faru a wasan da Fulham ta yi nasara kan Wolverhampton Wanderes da ƙwallaye 3 da 2 jiya Litinin ƙarƙashin gasar ta Firimiyar ya ja hankalin masharhanta bayan da alƙalin wasa Michael Salisbury ya amince da bugun fenariti ga Fulham a wajen da kowanne ɓangare…
Read More
Nijeriya na duba yiwuwar sallamar kocin Super Eagles

Nijeriya na duba yiwuwar sallamar kocin Super Eagles

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Ƙwallon Ƙafar Nijeriya ta fara laluben wanda zai maye gurbin mai horas da tawagar ƙwallon ƙafar ƙasar, Super eagles, Jose Peseiro, yayin da ta ke duba yiwuwar sallamar sa. Kwamitin gudarwar hukumar, ya ce bai gamsu da yadda kocin ke jagorantar Super Eagles ba, inda ya yanke shawarar nemo mai horaswa daga cikin gida. Tun lokacin da Kocin ɗan ƙasar Portugal ya karvi jagorancin ƙungiyar a shekarar 2022, wasanni shida kacal ya samu nasara a kai, inda ya yi rashin nasara a wasanni 15. Shugaban kwamitin, Shariff Ahlan yayin wata ganawa da manema labarai, ya…
Read More