Editor

9513 Posts
NUJ ta yi tir da cin zarafin ɗan jarida a Neja

NUJ ta yi tir da cin zarafin ɗan jarida a Neja

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Cikin makon da ya gabata ne Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro na jihar Neja, Manjo Janar Bello Mohammed Abdullahi (mai ritaya) ya ci zarafi, tare da tozarta wakilin gidan Radiyon Muryar Amirka na jihar Neja, Alhaji Mustapha Nasiru Batsari. Da ya ke nuna takaicin sa game da wannan lamari, Shugaban Ƙungiyar 'yan jarida ta qasa NUJ, reshen jihar Neja, Kwamared Abu Nmadu ya bayyana wannan abu a matsayin abin takaici. Abu Nmadu ya ci gaba da cewa sun kaɗu matuƙa da jin faruwar wannan lamari, wanda ya ce ba za su tava lamuntar irin wannan…
Read More
Masu aikata laifi a Filato, Benuwai da Nasarawa su shiga taitayinsu, inji rundunar AIG da aka tura

Masu aikata laifi a Filato, Benuwai da Nasarawa su shiga taitayinsu, inji rundunar AIG da aka tura

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sabon Mataimakin Sufeto Janar, AIG, mai kula da hedikwatar shiyya ta 4 da ke Makurdi, Mista Ebong Eyibio, ya yi gargaɗin cewa babu inda za a yi laifi a yankinsa. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a ranar Alhamis, mai xauke da sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan shiyya ta 4, PPRO, ASP David Kaavanger, kuma aka miƙa wa Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya a Makurdi. Mista Eyibio ya ce zai tabbatar da cewa masu aikata laifuka ba su da gurbi a…
Read More
Dakatar da bautar da ƙananan yara a Nijeriya

Dakatar da bautar da ƙananan yara a Nijeriya

Akwai wani al'amari mai matuƙar tayar da hankali da ban tausayi kan yadda ake amfani da yara masu ƙananan shekaru maza da mata don yin aiki ko bauta a gidaje da sauran wurare da suka haɗa da shaguna, otel-otel, wuraren kwana na manyan makarantu ko ɗakunan kwanan ɗalibai a jami’o’i. Akasarin yaran ’yan ƙasa da shekaru 15 ne kuma ana ɗaukarsu ne da nufin yin aikace-aikacen da suka haɗa da shara, wanke-wanke, wanki, goge-goge, ɗebo ruwa da rainon jarirai da kula da yayayyun yara da makamantansu. Mafi yawan yaran ana kawo su cikin birni daga ƙauyuka lokaci zuwa lokaci, ta…
Read More
Rashin adalci a shari’ar zaɓen Kano na iya haddasa tashin hankali – NNPP

Rashin adalci a shari’ar zaɓen Kano na iya haddasa tashin hankali – NNPP

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jam’iyyar adawa ta NNPP a Nijeriya ta ce hana ta ƙwace mata zaven da ta ci a jihar Kano, zai iya janyo tashin hankalin da zai yaɗu zuwa sauran ƙasahen Afirka. Wata sanarwa da muƙaddashin shugaban jam'iyyar na ƙasa, Abba Kawu Ali, ya fitar, kuma babban jami'i mai binciken kuɗi na jam'iyyar, Ladipo Johnson ya karanta a gaban ofisoshin jakadancin Ƙasashen Yamma ranar Laraba, NNPP ta yi iƙirarin cewa akwai alamun da ke nuna cewa ana yunƙurin yi wa zaɓen mafi rinjayen al'ummar Kano zagon ƙasa. 'Ya'yan jam'iyyar suna ci gaba da zanga-zanga a…
Read More
PDP ga majalisa: Ku yi watsi da ƙudirin kasafin 2024

PDP ga majalisa: Ku yi watsi da ƙudirin kasafin 2024

*”Akwai shifcin gizo da aringizo cikinsa” Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Babbar Jam’iyyar adawa a Nijeriya, PDP, ta roqi Majalisar Dokoki ta Ƙasar, wato Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai da cewa, kada su amince da kasafin kuɗi na 2024, domin cike ya ke maƙil da aringizo, almara da rainin hankali ga talakawa. Sakataren PDP na Ƙasa, Debo Ologunagba, ne ya fitar da wannan sanarwa a ranar Alhamis, kwan ɗaya bayan Shugaba Bola Tinubu ya kammala gabatar da kasafin a gaban gamayyar zauren Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya a Abuja a ranar Laraba. Kasafin na Naira Tiriliyan 27.5 dai PDP…
Read More
Super Eagles ta faɗo mataki na 42 a teburin FIFA

Super Eagles ta faɗo mataki na 42 a teburin FIFA

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Super Eagles ta Nijeriya ta yi ƙasa zuwa mataki na 42 a jerin waɗanda ke kan gaba a ƙwallon aafa a duniya, kamar yadda FIFA ta sanar. A jadawalin da FIFA ta fitar ranar Alhamis, Nijeriya ta ɓarar da maki 16.04, wadda ta haxa 1474.44, wadda ta ke da maki 1490.48 a cikin Oktoba. Sai dai wannan koma bayan bai shafi matakin Super Eagles a nahiyar Afirka ba, har yanzu tana nan a matsayi na shida. Biye da Moroko da Senegal da Tunisia da Algeria da kuma Masar a jerin waɗanda ke kan gaba a taka…
Read More
NDA ta rantsar da mutum 441 daga cikin sama da 30,000 da suka nemi gurbin karatu

NDA ta rantsar da mutum 441 daga cikin sama da 30,000 da suka nemi gurbin karatu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Cibiyar Horas da Sojoji ta Nijeriya (NDA) ta ƙi amincewa da sama da mutane 30,000 da suka nemi takardar shaidar kammala karatun digiri na 75 na babbar makarantar sojoji. Kwamandan NDA, Manjo Janar John Ochai, wanda ya bayyana haka a wajen taron karrama ɗalibai 441 da suka shiga cikin shirye-shiryen karatun digiri daban-daban a matsayin mambobin kwas na 75 na NDA, ya ce ɗalibai 441 da suka haɗa da ɗalibi ɗaya daga ƙasar Gambia an zaɓo su ne bayan kammala atisayen. Ya yi bayanin cewa zaɓar ɗalibai 441 kacal daga cikin sama da 30,000…
Read More
Jami’an ‘Civil Defence’ sun harbe ɗaliban sakandare a Abuja

Jami’an ‘Civil Defence’ sun harbe ɗaliban sakandare a Abuja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A ranar Laraba ne rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta kama tare da tsare wasu jami’an hukumar tsaro ta farin kaya da Sibil Difence guda uku bisa laifin harbe wasu ɗalibai biyu na babbar makarantar sakandare da ke unguwar Life Camp a unguwar Jabi da Gwarinpa a babban birnin tarayya. Jaridar ta rawaito cewa ɗaliban biyu da jami’an NSCDC suka harbe a halin yanzu suna karɓar kulawa a asibitin Gwarinpa. Bayan harbin, wasu ɗaliban makarantar sakandare da suka fusata sun lalata motocin sintiri uku na hukumar NSCDC domin nuna adawa da harin da aka kai…
Read More
’Yan N-Power sun koka da jinkirin biyan alawus da gwamnati ke yi

’Yan N-Power sun koka da jinkirin biyan alawus da gwamnati ke yi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu dake cikin shirin tallafi na N-Power a ranar Litinin sun koka kan jinkirin rashin biyansu alawus ɗin Naira 30,000 ɗin da gwamnati ke biyansu duk wata. Masu amfana da shirin sun koka da haka ne ganin yadda suka ɗauki tsawon watanni ba a biya su ba. Wani Francisco Noah dake cikin shirin Zango C1 ya ce yana koyarwa ne a makarantar makiyaya dake Keffi jihar Nasarawa ya ce rashin biyansu alawus ɗin ya hana shi zuwa wurin aiki. “Rajistan da na yi na shekara biyu wanda ya kamata a wannan watan Disamban da…
Read More
Kwanaki 70 ɗaliban Jami’ar Gusau ba su shaƙi iskar ‘yanci ba

Kwanaki 70 ɗaliban Jami’ar Gusau ba su shaƙi iskar ‘yanci ba

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Sama da watanni biyu da suka gabata ’yan bindiga da dama sun kai farmaki ƙauyen Gidan Dawa da ke kusa da Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta Gusau jihar Zamfara, inda suka yi garkuwa da mutum 28, ciki har da ɗalibai mata  na jami’ar, amma har yanzu 12 daga cikinsu su na hannun ’yan ta'addan, sun ƙi sakin su. Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Mu’azu Abubakar Gusau, a wata hira da manema labarai a watan da ya gabata ya tabbatar da cewa, har yanzu ɗalibai 12 na hannun ’yan ta'addar. A cewarsa, cikin mutane 28 da aka yi…
Read More