Editor

9513 Posts
HOTUNA: Babban Hafsan Sojoji ya jagoranci yi wa waɗanda suka mutu a harin Kaduna addu’a

HOTUNA: Babban Hafsan Sojoji ya jagoranci yi wa waɗanda suka mutu a harin Kaduna addu’a

Babban Hafsan Hafsoshin Sojin Nijeriya, Lt. General Taoreed Lagbaja, ya jagoranci yin addu'a ga gomman waɗanda suka rasa rayukansu a harin kuskuren da jirgin saman soji mara matuƙi ya kai a Tudun Biri cikin Ƙaramar Hukumar Igabi, Kaduna a ranar Lahadi. Rundunar Sojojin Nijeriya Nijeriya ta ɗauki alhakin kai harin, inda ta ce hakan ya faru ne a bisa kuskure. Ga ƙarin hotuna:
Read More
Harin Kaduna: Tinubu ya bada umarnin gaggauta gudanar da bincike

Harin Kaduna: Tinubu ya bada umarnin gaggauta gudanar da bincike

*Adadin waɗanda suka rasu ya ƙaru Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bada odar gudanar da cikakken bincike kan harin da jirgin sojin Nijeriya mara matuƙi ya kai Jihar Kaduna inda ya kashe gomman farar hula. Tinubu ya kuma jajanta wa 'yan uwa da Gwamnatin Jihar Kaduna game da waɗanda suka mutu da waɗanda suka jikkata a harin wanda ya auku a Tudun Biri cikin yankin Ƙaramar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna. Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Ajuri Ngelale, ya fitar da safiyar ranar Talata. Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu…
Read More
Kwanaki 16 na gangamin yaƙi da tauye haƙƙoƙin mata

Kwanaki 16 na gangamin yaƙi da tauye haƙƙoƙin mata

Tare da ABBA ABUBAKAR YAKUBU Ƙungiyoyin mata a ko'ina a faɗin duniya, na gudanar da wani gangamin wayar da kan al'umma game da yaƙi da cin zarafin mata da tauye musu haƙƙoƙin su a fuskar shari'a, shugabanci, siyasa, da zamantakewa. Wannan gangami na tsawon kwanaki 16 wanda ake yi wa laƙabi da Orange the World a Turance, yana mayar da hankali ne wajen tattauna yadda za a kawo ƙarshen wasu matsaloli 16 da manyan mata da ƙananan yara mata ke fuskanta a cikin al’ummomi daban-daban na duniya. Gangamin na so ne a kawo ƙarshen wulaƙanta mata a gidajen aure. A…
Read More
Kotu ta bada umarnin ƙwace motocin gwamnati da Bello Matawalle ya yi awon gaba da su

Kotu ta bada umarnin ƙwace motocin gwamnati da Bello Matawalle ya yi awon gaba da su

Daga BASHIR ISAH Babbar Kotun Tarayya mai zamanta a Sakkwato ta yi watsi da ƙarar da tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya shigar game da mallakar motocin gwamnati da ya yi awon gaba da su. A watan Yunin da ya gabata 'yan sanda a Jihar Zamfara suka kai samame gidan tsohon Gwamna Matawalle inda suka ƙwace motocin gwamnati da ke jibge a gidan bisa umarnin kotu. Sanarwa daga Kakakin Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ta ce Babbar Kotun Tarayya mai zamanta a Sakkwato ta yi watsi da iƙirarin Bello Matawalle kan cewa motocin da ake magana mallakinsa ne. A…
Read More
Dandalin shawara: Iyayena sun kai ni gidan mai mata huɗu a matsayin barwa da ya siya (4)

Dandalin shawara: Iyayena sun kai ni gidan mai mata huɗu a matsayin barwa da ya siya (4)

Ƙarshen wannan tambaya Daga AISHA ASAS TAMBAYA: Anti Aysha Asas ina yini, ya lamura? Don Allah kar ki ambaci sunana, ko garin da nake. Wallahi na matsu ne, shi ya sa zan fallasa wannan sirrin don Ina son na samu mafita, saboda yanzu kaina ya yi zafi kan lamarin, ban san inda zan fuskata ba. Ina da shekara sha uku, uwata da kawuna da mai unguwarmu da wanda uwata take zaune gida nai, tana taya matansa aiki, suka shirya da ni, muka taho cikin garin………….da kayana da komai nau. Muka taho gidan wani babban mutum da yake da mata huɗu,…
Read More
Idan ka na sana’a ba ka da wannan tunani, kai da cigaba sai a mafarki – Likitan sana’a

Idan ka na sana’a ba ka da wannan tunani, kai da cigaba sai a mafarki – Likitan sana’a

Daga AMINA YUSUF ALI Malam Badamasi Aliyu Abdullahi masani ne a kan dabarun tafiyar da sana'a da tattalin arziki. Ga wasu shawarwari da ya bayar a kan sana'a kamar haka: Son koyo  da neman ilimi. Masu sana'a da ke da aƙida ta son cigaba suna son koyo ko sanin wani sabon abu da ya danganci harkar sana'arsu. Sun yarda cewa duniya kullum cigaba ake samu kuma cigaba a harkokin kasuwanci yana da kyakkyawar alaƙa da neman ilimi sana'a, fahimtar tattalin arziƙi, fahimtar ƙudurorin gwamnati, koyon amfani da sabbin dabaru, sabbin kayan aiki da sauransu.  2. Kallon ƙalubale a matsayin taki.…
Read More
Duk da alƙawarin SDG, nakasassu na fuskantar tsangwama — Antonio Guterres

Duk da alƙawarin SDG, nakasassu na fuskantar tsangwama — Antonio Guterres

Daga BASHIR ISAH Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres, ya jaddada muhimmancin tafiya tare don cimma Manufofin Cigaba Mai Ɗorewa (SDG), musamman don bunƙasa rayuwar nakasassu biliyan 1.3 a faɗin duniya. Sakataren ya ce, “Ranar Nakasassu ta Duniya ta bana tuni ne gare mu cewa domin cimma manufofin SDG hakan na buƙatar a tafi tare, musamman inganta rayuwar nakasassu biliyan 1.3 a faɗin duniya." Guterres ya bayyana haka ne a ranar Lahadi, 3 ga Disamban 2023 domin bikin Ranar Nakasassu ta Duniya. “A yau, kuma a matsayin kama hanyar cimma Ƙudirin 2030, nakasassu na ci gaba da fuskantar tsangwama…
Read More
Kotun Ƙoli: Lauyoyi sama da 200 sun lashi takobin mara wa Gwamnan Kano baya

Kotun Ƙoli: Lauyoyi sama da 200 sun lashi takobin mara wa Gwamnan Kano baya

Daga BASHIR ISAH Aƙalla sama da lauyoyi 200 masu zaman kansu daga Arewa ne suka bayyana ƙudirinsu na taimaka wa Gwamna Abba Kabir na Jihar Kano domin ganin ya yi nasara a Kotun Ƙoli bayan ɗaukaka ƙara da ya yi. Lauyoyin ƙarƙashin ƙungiyarsu ta Abba Kabir Yusuf Volunteer Lawyers Forum For The 19 Northern states And Abuja, sun bayyana aniyarsu ta mara wa Gwamna Abba baya ne a taron manema labarai da suka shirya a Arewa House ranar Lahadi a Kaduna. Mai magana da yawun lauyoyin, Yusuf Ibrahim, sun yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Kotun Ƙoli…
Read More
Kasafin Naira Tirilyan 27 na 2024 ya cika tirela

Kasafin Naira Tirilyan 27 na 2024 ya cika tirela

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Haƙiƙa ko dai yawan tarin takardun kuɗin da su ka kai Naira Tirilyan 27 ba su cika babbar motar ɗaukar kaya wato tireba ba to za su dai cika waje mai faɗin gaske a motar. Ko ni mai rubutun nan ban tava ganin Naira tirilyan a kan takarda ba. Naira tirilyan na nufin Naira biliyan 1000. Naira biliyan na nufin Naira miliyan 1000. Naira miliyan na nufin Naira dubu ɗari sau 10. Kawai na kiyasta ne yadda yawan kuɗin su ke in an zuba su a ɗaki ko a cikin mota. A watannin baya kafin…
Read More
Mu guji cusa ƙiyayya a tsakanin jama’a

Mu guji cusa ƙiyayya a tsakanin jama’a

Assalamu alaikum, da fatan kowa muna lafiya, ameen. Mu sani cewa, kowane mutum da Allah ya yi, ya yi shi da irin nasa tunanin, kowa da yadda yake kallon abu idan ya zo masa, kamar yadda yake kuma kowa da irin nasa ra’ayin. Wasu ana iya kawar da su daga kan ra’ayinsa mummuna ko kyakkyawa, wasu kam ba yadda za a yi a iya kawar da su daga ra’ayin da suka ginu a kai. Irin wannan ra’ayi da fahimta da Allah ya yi kowa tasa daban, shi ne ya kamata a ce kowa ya tsaya a kan nasa, kada wani…
Read More