Dandalin shawara: Iyayena sun kai ni gidan mai mata huɗu a matsayin barwa da ya siya (4)

Ƙarshen wannan tambaya

Daga AISHA ASAS

TAMBAYA:

Anti Aysha Asas ina yini, ya lamura? Don Allah kar ki ambaci sunana, ko garin da nake. Wallahi na matsu ne, shi ya sa zan fallasa wannan sirrin don Ina son na samu mafita, saboda yanzu kaina ya yi zafi kan lamarin, ban san inda zan fuskata ba.

Ina da shekara sha uku, uwata da kawuna da mai unguwarmu da wanda uwata take zaune gida nai, tana taya matansa aiki, suka shirya da ni, muka taho cikin garin………….da kayana da komai nau. Muka taho gidan wani babban mutum da yake da mata huɗu, sai a gidan wanda uwata take zaune wurin sa ya ce, wai ni baiwa ce, kuma mutumin ne ya siye ni daga hannunsa. Kuma zan zauna da shi matsayin matarshi.

Nan na zauna cikin tsangwama, ba mai shiga sha’anina daga matanshi ko dangi, suna ƙyama ta, ko shi kamar yana ɓoye ni a wajen mutane, bai cika faɗa wa mutane ko ni wacce ce ba. Haka na haihi ɗiya har guda huɗu, sannan kuma Ina zuwa makaranta ta Allah, ana mana karatun Ƙur’ani da sauransu. To shi ne kwanaki mallam yake bayani sai ya yi maganar babu bayi, ɗiya ne ake ta saye, ana zaman zina da su.

AMSA:

ko ta wannan hangen za ki iya samun kaso mai yawa daga amsar da ki ke nema. Ina zancen idan har kin aminta har yanzu da ragowar bayi. Idan har kin ga kamani ko ɗaya daga cikin tambayoyin da muka zayyano a makon jiya a vangaren biri ya yi kama da mutum, zan iya cewa, akwai wani batu da muka ji a kwanakin baya, kan sha’anin yadda wasu ke amfani da tarihi suna mayar da ‘ya’ya bayi.

Lamarin ya nuna cewa, asalin bayin a lokacin da aka haramta bautar, sai ya kasance ba a samun bayi a ko’ina sai a gidajen ‘yan siyasa ko masu mulki.

A irin wuraren za ka tarar da bayi masu yawa da ke hidimta masu maza da mata, tafiya da ta yi tafiya, sai ‘ya’yan gidan da kuma na maqwabta suka dinga harin waɗannan bayin, suna kwana da su.

Kawai za ka ga baiwarka da ke hidimta maka, kuma kai ba ka killace ta ba, sai ka ganta da ciki, kuma kai da ka mallake ta ba ka ajiye ta don hakan ba, to irin wannan yanayi sai su kawar da kai, su ƙi yin abinda ya dace, wato bincikar wanda ya yi cikin, sai su bar shi a matsayin ƙari suka samu a cikin bayin nasu, wato su ajiye ɗan a matsayin bawa.

Wannan na ɗaya daga cikin dalilan da ke sa ake ganin gaurayyar jinsi a tsakanin waɗanda ake iƙrarin bayi ne, ma’ana idan a baya duk bayin da ke gari kaza baƙaƙe ne, saboda kasancewarsu daga jinsin baƙaƙe da bauta ce kawai ta kawo su garin, sai ya kasance a wayi gari an gabatar da farin mutum a matsayin bawa, kuma alhali duk garin babu bawa a cikin jinsin nasu, to ya akai ta samu ɗa fari? Idan kuwa duk fararen ‘yantattu ne to tabbas ɗan ba zai zama bawa ba.

Haka kuma za ka iya samun wata ƙabila da aka ciwo yaƙi, aka mayar da ragowarsu bayi, sai kaga a cikinsu sun haifi yara da kamani na waɗanda ke bautar da su. To ta yaya hakan za ta kasance idan ba su ne da cikin ba. Duk waɗannan da na zayyano ba bayi ba ne kamar yadda na faɗa a baya. Kinga kuwa ko ta nan kawai an gurvata sahihancin bayi.

Baya ga waɗannan tambayoyi da za su iya fitar da ke duhu, za ki iya faɗaɗa bincike a wurin malamai, wanda idan na fahimce ki daidai kina da damar yin hakan tunda kina fita. Kuma baya ga wannan a matsayin ki ta wadda ta mallaki hankalinta a yanzu, za ki iya bin didigin asalin naki daga wurin iyaye, ki cike wuraren da babu rubutu na daga rayuwarki, daga nan sai ki ƙara da hujjojin da za ki iya samu daga wurin malamai.

Idan da ba don ƙoƙarin da ki ke yi na ki warware lamarin cikin sirri ba, wanda zan iya cewa na fahimce ki sosai ko don ‘ya’yan naki za ki so hakan, da zan iya cewa, akwai babban malamin da zan iya haɗaki da shi a nan inda ki ke, da nake da tabbacin zai iya yin mai yiwa don ganin an cimma matsaya da ta dace da addininmu.

Sai dai duk da haka, kin fi duk wanda yake da iko kan wannan lamari ƙarfi, domin gwamnati da ƙungiyoyi da dama na aikin ganin ba a yi maki abinda aka yi maki ba. Sai dai kafin komai ya kamata ki samu nutsuwa kan hallaci ko haramcin zaman da ki ke yi, kuma yadda na faɗa maki ne hanyar da za ki iya bi cikin sirri ki samu amsa, ko malaman ba dole sai kin masu bayyanin ke ce ba, domin za ki iya cin karo da masu sauqin baki.

Idan kuwa kin samu tabbaci kina neman ɗaukar mataki na gaba, don kaucewa matsayin da ki ke kai, ko kuma cin cire tsoron yiwar sirrin naki ya fallasa, kina son ɗaukar mataki a hukumance, to ki sake tavo ni, don ba ki taimakon da ya dace.

Daga qarshe, ki saka Allah a gaba, ki nemi zavi da taimakonSa kafin na kowa, ki roƙe Shi ya bayyana maki hanya madaidaiciya da ya kamata ki bi kan wannan lamari, sannan Ya sawwaƙe maki hanyoyin da zaki bi, Ya kuma rufe sirrin don ‘ya’yan da ki ke da su.

Wanda ya dogara ga Allah, ba zai taɓa kunyata ba.