Idan ka na sana’a ba ka da wannan tunani, kai da cigaba sai a mafarki – Likitan sana’a

Daga AMINA YUSUF ALI

Malam Badamasi Aliyu Abdullahi masani ne a kan dabarun tafiyar da sana’a da tattalin arziki. Ga wasu shawarwari da ya bayar a kan sana’a kamar haka:

  1. Son koyo  da neman ilimi. Masu sana’a da ke da aƙida ta son cigaba suna son koyo ko sanin wani sabon abu da ya danganci harkar sana’arsu. Sun yarda cewa duniya kullum cigaba ake samu kuma cigaba a harkokin kasuwanci yana da kyakkyawar alaƙa da neman ilimi sana’a, fahimtar tattalin arziƙi, fahimtar ƙudurorin gwamnati, koyon amfani da sabbin dabaru, sabbin kayan aiki da sauransu.

 2. Kallon ƙalubale a matsayin taki. Me sana’a da ke son ya yi nasara a kasuwanci, sai ya daina tsoron ƙalubalai. Fuskantar matsaloli a kasuwanci dole ne. Misali yanzu babban abinda ke damun masu sana’a shi ne hauhawar farashi a kasuwa. Me sana’a da ke da aƙidar son cigaba, yana kallon ƙalubale ne a matsayin taki na cigaba domin ya san duk abinda ba kalubale a ciki to babu tasirin canji mai ƙarfi a cikinsa. A maimakon a sare ko a karaya, tunani ake a ga wace hanya za a bi a shawo kan ƙalubalen da ya taso.

  1. Iya gano damarmakin kasuwanci da sana’a. Masu aƙidar son cigaba, a duk inda su ke, idanun su a buɗe suke don ganin sabbin damarmaki da dabarun cigaba kasuwancinsu. Sun fahimci cewa, duk inda ɗan Adam ke rayuwa, akwai damarmakin kasuwanci da sana’a da kuma samun arziƙi. Inda mutane ke rayuwa, akwai buƙatu na neman ilimi, sutura, abinci, sufuri, muhalli, lafiya, tsaro, nishaɗi da sauransu. Kan me aƙidar son cigaba, ba ya kullewa ya zo yana vabatun babu opportunities a gari. Daukar laifi. Masu Growth Mindset suna da abinda ake kira sanin darajar kai. Idan ba su tsaya sun inganta sana’arsu ba, ba su ƙara mata daraja ba, ba su tsara strategies na tallata hajarsu ba, ba su kyautawa kwastomominsu ba, to fa in sana’arsu ko kasuwancinsu ya ƙi cigaba, ba za su ɗorawa shugaban ƙasa ko gwamna ko tattalin arziƙi laifi ba.  Masu sana’a da ke da aqidar son cigaba, idan kuskure na su ne, ba sa ɗorawa kowa laifi. Karɓar laifinsu suke, su gyara.

 5. Neman mafita. Na biyar shi ne neman mafita. Masu sana’a da ke da aƙidar son cigaba, kullum tunanisu na ginuwa ne a kan neman mafita. Idan suna fama da rashin wuta, tunanin su wacce hanyar za su bi, su samawa kansu mafita. Idan ba sa samun ciniki, sai su yi ta nazarin menene mafita. Duk matsalar da ta sa su a gaba, tsayawa su ke su yi tunani, su nemi shawara, su yi bincike a kan mafita. Abin lura a nan shi ne masu aqidar son cigaba, ba sa tsayawa su yi ta qorafi akan matsala. Amfani su ke da lokacin su wajen neman mafita.

Badamasi Aliyu ya qara da cewa, idan kuma sana’arka ta dandalin soshiyal midiya ce, ga dabarun da za a bi a bunƙasa ta:

  1. Farfajiyar dandalin soshiyal midiya. Idan ka na sana’a, ka tabbatar ka tsaftace Farfajiyar dandalin soshiyal midiya ɗinka. Ya kasance daga shigowa profile ɗinka, mutum ya fahimci me ka ke siyarwa ba tare da vata lokaci ba. Akwai abinda ake kira bounce rate” a kasuwancin yanar gizo Wannan ma na nufin daɗewar da mutane suke yi idan sun shigo shafinka. Da zarar ba su ga wani abu mai amfani ko da ya burge su ba, za su fice. Kuma in sun fice ba za su ƙara dawowa ba.
  2. Shafin yanar gizo: Ana so ka buɗe asusun yanar gizo guda biyu aƙalla. Da naka na ƙashin kai da kuma shafi na kasuwanci. Tun asali,  Fesbuk (Meta a yanzu), sun ba da damar buɗe shafin kasuwanci ne saboda a nan suke so ‘yan kasuwa su riƙa tallata hajojinsu. Wannan ya sa a da, ake cewa Farfajiyar dandalin soshiyal midiya.  A yau dai hakan ya canza, domin tasirin furofayil na ƙashin kai wajen tallata sana’a cikin salo na wayo ya fi na shafika. Amma ba kowa ne ya san hakan ba. Wataƙila nan gaba na ɗan yi sharhi a kai a wani rubutun.
  3. Comment marketing. Duk mai sana’a da ke amfani da Facebook, yana da kyau ya ke amfani da wannan dabarar. Kasuwancin cikin kwamen shi ne tsayawa ka rubuta kwamen me ma’ana. Wannan dama ce babba da ta ke janyo hankalin mutane kanka. Su gane cewa lalle in har za ka iya yin wannan kwamen ɗin a ƙarƙashin wallafar wani, to lallai ka na da ƙarfin yin abinda ya fi haka a shafin ka. Masu wayo da su ka naƙalci kasuwancin soshiyal midiya, na amfani da wannan wajen ciyar da kasuwancinsu gaba.
  4. Shiga guruf-guruf na masu sana’a. Fesbuk sun ba da damar buɗe tare da shiga guruf-guruf ne saboda mu’amala da mutane masu yawa da ra’ayin suya zama ɗaya. Kowane irin kasuwanci ka ke, akwai guruf na wannan kasuwancin a Fesbuk. Ya rage naka ka yi bincike, ka shiga. Idan kuma babu, kai sai ka buxe, ka yaɗa sanarwa don masu sana’a irin ta ka, su samu damar shiga. Yana da kyau ka je ka yi bincike a kan irin gudunmawar da guruf-guruf suke bayarwa a cigaban kasuwanci a Fesbuk.