Duk da alƙawarin SDG, nakasassu na fuskantar tsangwama — Antonio Guterres

Daga BASHIR ISAH

Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres, ya jaddada muhimmancin tafiya tare don cimma Manufofin Cigaba Mai Ɗorewa (SDG), musamman don bunƙasa rayuwar nakasassu biliyan 1.3 a faɗin duniya.

Sakataren ya ce, “Ranar Nakasassu ta Duniya ta bana tuni ne gare mu cewa domin cimma manufofin SDG hakan na buƙatar a tafi tare, musamman inganta rayuwar nakasassu biliyan 1.3 a faɗin duniya.”

Guterres ya bayyana haka ne a ranar Lahadi, 3 ga Disamban 2023 domin bikin Ranar Nakasassu ta Duniya.

“A yau, kuma a matsayin kama hanyar cimma Ƙudirin 2030, nakasassu na ci gaba da fuskantar tsangwama da wariya wanda ke hana su ‘yancin yi da su a dukkanin ɓangarori na harkokin al’umma.”

Ya kuma nuna muhimmancin nakasassu wajen bunƙasa tattalin arziki da harkokin siyasa, maimakon kallon mutanen ba sa bada kowace gudummawa ga cigaban al’umma kamar yadda wasu ke yi musu kallo.

Yana mai cewa, “Wannan na nufin a riƙa yi da nakasassu wajen ɗaukar matakan cigaba da aiwatar da su daidai da Dokar Kare ‘Yancin Nakasassu.

“Kuma ana ci gaba da ƙoƙari a ƙasashen duniya domin ganin yadda za a cimma manufofin SDG, kama daga kawar da talauci zuwa kyautata sha’anin kiwon lafiya da ilimi mai inganci” da sauransu.

Guterres ya yi kira ga ƙasashen duniya a bada himma tare da haɗa kai da nakasassu wajen tsare-tsare da aiwatar da su don bai wa kowa ‘yanci.