07
Dec
Daga BASHIR ISAH Wasu mata a garin Zariya, Jihar Kaduna, sun gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna ɓacin ransu dangane da harin soji da ya faɗa kan masu maulidi a ƙauyen Tudun Biri da ke Ƙaramar Hukumar Igabi a jihar. An ga masu zanga-zangar sun yi tattaki a cikin garin na Zaria ɗauke da kwalaye masu ɗauke da saƙonni daban-daban kamar; "Adalci ga Arewa", "Adalci ga Igabi" da sauransu. Sama da mutum 80 ne suka mutu sannan wasu da dama sun tagayyara sakamakon harin da sojoji suka jefa bom har sau biyu ta hanyar amfani da jirgin sama mara matuƙi…
