Editor

9513 Posts
’Yan bindiga sun sake sace ɗaliban jami’ar Nasarawa

’Yan bindiga sun sake sace ɗaliban jami’ar Nasarawa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wasu ’yan ta'adda da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne sun afka wa al’ummar Gandu tare da yin garkuwa da wasu ɗalibai a Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Lafia. Wani ɗalibin jami’ar da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa manema labarai cewa 'yan bindigar sun zo ne da farko a yawansu da misalin ƙarfe 7:30 na yammacin ranar Laraba inda suka fara harbi a iska don tsoratar da mazauna yankin, amma daga baya sun fara harbi kan mai uwa da wabi, lura da cewa jami'an tsaro na tahowa sai suka tsere cikin daji domin…
Read More
Babu wata matsala a Man United – Ten Hag

Babu wata matsala a Man United – Ten Hag

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kocin Manchester United Erik ten Hag ya yi watsi da raɗe-raɗin cewa an samu rabuwar kai a Old Trafford, yana mai jaddada cea ƙungiyar na tafiya kan turbar da ta dace. Da ƙwallo biyun da Scott McTominay ya zura a ragar Chelsea a wasan da suka tashi 2-1 ranar Talata, shi ne karon farko da ƙungiyar ta Ten Hag ta ci wata ƙungiya da ke cikin goman farko a Firimiya da ake yi yanzu. Kocin ya ce da Manchester sun yi amfani da damar da suka samu a wasan da bai wahalar da su ba kamar…
Read More
Kotu ta yanke hukuncin kisa kan matashin da ya kashe abokinsa saboda N100 a Zamfara

Kotu ta yanke hukuncin kisa kan matashin da ya kashe abokinsa saboda N100 a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Wata Babbar Kotun Jihar Zamfara ta yanke wa wani Anas Dahiru hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsa da laifin kashe abokinsa a kan Naira 100. An gurfanar da Dahiru kotu ne a watan Yunin 2017 bisa zargin kashe abokinsa Shamsu Ibrahim inda ya daɓa masa wuƙa har lahira a lokacin da suke faɗa da juna saboda Naira 100. Da yake karanta hukuncin, Alƙalin Kotun, Mai shari’a Mukhtar Yusha’u ya ce wanda ake zargin Anas Dahiru da ke Unguwar Dallatu a garin Gusau a Jihar Zamfara, ya gurfana a gaban kotu a shekarar 2017 bisa…
Read More
Za a shiga mummunan bala’i a Gaza idan ba ku ɗauki mataki ba – MƊD

Za a shiga mummunan bala’i a Gaza idan ba ku ɗauki mataki ba – MƊD

Daga WAKILINMU Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya (MƊD), Antonio Guterres, ya rubuta wasiƙa ga kwamitin tsaro na majalisar, inda ya nemi ƴan kwamitin su taimaka don kauce wa mummunar annoba a Gaza. "Yayin da ake fuskantar shiga bala'in rasa agaji a Gaza, ina neman Kwamatin ya taimaka wajen kauce wa aukuwar bala'i, kuma ya nemi a tsagaita wuta don kai agaji," in ji Guterres a cikin wani saƙo da ya walafa ranar Laraba. Cikin wasiƙar da ya rubuta, Guterres ya nanata cewa yanayin na ƙara ƙazancewa cikin sauri, ta yadda ba za a iya gyara wa Falasɗinawa komai ba…
Read More
Harin bom: Shettima ya ziyarci Kaduna don jajanta wa al’ummar Tudun Biri

Harin bom: Shettima ya ziyarci Kaduna don jajanta wa al’ummar Tudun Biri

Daga BASHIR ISAH Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, ya ziyarci Jihar Kaduna domin jajanta wa 'yan uwan waɗanda harin bom da sojoji suka kai bisa kuskure ya rutsa da su a yankin Tudun Biri a jihar. Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani da sauran manyan jami'an gwamnati ne suka tarbi Mataimakin Shugaban Ƙasar bayan da ya sauka a barikin sojojin saman da ke Mando. Tawagar da ta yi wa Shettima rakiya zuwa Kaduna a ranar Alhamis ta ƙunshi Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajuddeen, Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar; Shugaban APC na Ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje da dai sauransu. Ziyarar Shettima…
Read More
BESDA: Gwamna Lawal ya jagoranci tawaga zuwa taron bita a Rwanda

BESDA: Gwamna Lawal ya jagoranci tawaga zuwa taron bita a Rwanda

Daga BASHIR ISAH Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jagoranci tawaga ta musamman zuwa Kigali don taron bita na yini huɗu a matsayin ɓangare na kammala shirin ba da nagartaccen ilimi na Better Education Service Delivery for All (BESDA) a jihar. Bitar mai ƙunshe da ayyuka daban-daban, an soma ta ne daga ranar Litinin, 4 ga Disamba, da zummar farfaɗo da fannin ilimin Jihar Zamfara. Mai magana da yawun Gwamna, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana a cikin sanarwar da ya fitar cewa, shirin BESDA shiri ne na Bankin Duniya wanda aka ƙirƙiro da nufin bunƙasa sha'anin ilimi da kuma bai…
Read More
Abinda mata suke so a wajen maza!

Abinda mata suke so a wajen maza!

Daga AMINA YUSUF ALI Barkanmu da sake haɗuwa a wani makon a filinmu na zamantakewa daga jaridarku mai farin jin ta Blueprint Manhaja. Kamar yadda a baya muka yi maƙala a game da abinda maza ke so gurin mata. A wannan makon kuma muna tafe da tambayar wai me mata suke so wajen maza? Tambayar nan mai tsauri ce kuma mai faɗi kamar dai maudu'inmu na makon da ya gabata. Wato wai me maza suke so a wajen mata? Inda muke sa ran shi ma na wannan makon za mu yi sukuwa mu yi zamiya mu cimma matsaya kamar makon…
Read More
Marubuta na taka muhimiyyar rawa a zamantakewar aure – Binta Umar Abbale

Marubuta na taka muhimiyyar rawa a zamantakewar aure – Binta Umar Abbale

"Marubuta na fuskantar ƙalubalen satar fasaha" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Marubuta mutane ne masu martaba da kwarjini, waɗanda Allah Ya yi wa bai wa ta abubuwa daban-daban da suke amfanar da jama'a. Binta Umar Abbale na daga cikin irin marubutan da jama'a da dama ke ƙaruwa da ita. Bayan kasancewarta marubuciya, ƴar kasuwa, tana kuma bada shawarwari ga mata ta yadda za su gyara kansu da zamantakewar aurensu. Binta Abbale wacce ita ce shugabar ƙungiyar marubuta ta Manazarta Writers Association ta rubuta littattafai 19 da suka ƙunshi labarai masu ɗauke da darussa na faɗakarwa da nishaɗantarwa. A ganawarta da wakilin…
Read More
Bincike da karatu suka sa ake min kallon ba ’yar Arewa ba – Maryam Bichi

Bincike da karatu suka sa ake min kallon ba ’yar Arewa ba – Maryam Bichi

“Nasara ce yadda mutane ke kallo na a matsayin mafita ga al'umma" Daga MUHAMMADU MUJITTABA, a Kano  Matashiya Maryam Bichi, 'yar gwagwarmaya akan ilimin kasuwanci da fasahar sadarwa da bunƙasa kasuwancin zamani ta hanyar ilimantar da al'umma maza da mata da burinta na zama tauraruwa daga matan Arewa da ta kafa makarantar fasahar sadarwa a rayuwarta da dai sauran bayanai masu mahimmanci na ƙalubale da nasarorin da ta samu a rayuwarta ta shekaru 29 a duniya. Wakilinmu ya samu zantawa da matashiyar, don haka ku biyo mu don jin yadda tattaunawar ta kasance. MANHAJA: Za mu so mu ji wacce…
Read More
An buƙaci Tinubu ya tsige shugabannin tsaro biyo bayan harin bom a Kaduna

An buƙaci Tinubu ya tsige shugabannin tsaro biyo bayan harin bom a Kaduna

Daga BASHIR ISAH Ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta yi kira da a tsige manyan shugabannin sojoji kan harin bom da sojoji suka kai bisa kuskure a Tudun Biri, Jihar Kaduna, wanda hakan ya salwantar da rayuka sama da 85 tare da jikkata wasu da dama. Mai sharhi kan al'amuran yau da kullum kuma mamba a ƙungiyar NEF, Farfesa Usman Yusuf, shi ne ya yi wannan kira yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a tashar Channels Television a ranar Talata. Yusuf said, “Wannan rashin dacewa ne. Dukkansu za yi murabus, a kori duk wani jami'in da ke daga cikin…
Read More