09
Dec
Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau Dakarun rundunar haɗin guiwa ta arewa maso yammacin Najeriya Operation Hadarin Daji (OPHD) sun daƙile harin da 'yan ta'adda suka kai kauyen Danjibga dake ƙaramar hukumar Tsafe tare da daƙile ɓarnar amfanin gona a ƙauyen Faru dake ƙaramar hukumar Maradun duk a jihar Zamfara inda suka samu nasarar Kashe wasu da dama a batakashin da suka yi. Sojojin sun ce a yayin arangamar da ‘yan ta’addan sun samu nasarar hallaka guda uku daga cikin 'yan ta'addan, an kuma ƙwato bindigogi kirar AK-47 guda 3, kwanson alburusai 3, da kuma babura biyu. "A ranar 7 ga…
