Editor

9364 Posts
Iyaye a Arewa ku ji tsoron Allah kan sauke haƙƙin yaranku

Iyaye a Arewa ku ji tsoron Allah kan sauke haƙƙin yaranku

Assalamu alaikum, Manhaja. Barkan ku da aiki, muna muku fatan Allah ya ƙara muku ƙwazo, Ameen. Ina kuma muku addu’a Allah ya ƙara muku hikima da basirar aiki da kuma bunƙasa wannan jarida mai farin jini baki ɗaya. A Arewa ne za ka samu gidan Almajirai da yara ba adadi, a Arewa ne za ka samu iyaye sun sake yaran su ana kwashewa ana sauya musu addini, a Arewa ne za ka samu gidan kangararru inda ake tara ɗaruruwan yara wai da sunan sun gagari iyayensu. Kwanaki kaɗan da suka wuce wata baiwar Allah ta saka wani bidiyo a shafin…
Read More
APC, zaɓe ko naɗi?

APC, zaɓe ko naɗi?

Ban ce jam'iyya mai mulki APC na da tasirin mamaye duka faɗin ƙasarmu ba. Amma dai ga alamu har yanzu ta na da tasiri wajen samun magoya baya idan ta je zaɓe. Zaɓen ranar 11/11/2023 wanda aka gudanar a jihohin Bayelsa, Kogi, Imo tun kafin aje ranar ban hango ma APC rasa jihohin duka ba musamman yadda sau da dama ta ke ƙoƙari wajen nemo 'yan takara fitattu masu jama'a ta tsayar wanda ta hakan ta ke shammatar jam'iyyun adawa aje zaɓe su zamo yan kallo. Mu kula da kyau, har kullum ita siyasa abu ce mai buƙatar zurfafa tunani…
Read More
Boko Haram sun kai wa ayarin motocin Gwamnan Yobe hari

Boko Haram sun kai wa ayarin motocin Gwamnan Yobe hari

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu Wata majiya mai ƙarfi ta ce wasu mahara da ake kyautata zaton Boko Haram sun farmaki ayarin motocin Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni a kan hanyar su daga Maiduguri zuwa Damaturu bayan halartar taron yaye ɗalibai karo na 24 da Jami’ar Maiduguri ta shirya. Gwamna Buni ya kasance a Maiduguri tare da manyan baƙin da suka halarci bikin, amma daga bisani ya zarce zuwa Abuja domin gudanar da wasu muhimman ayyuka a can. Majiya ta tabbatar wa wakilinmu cewa, kwambar motocin jami’an tsaron sun yi arangama da Boko Haram tsakanin Jakana zuwa Mainok…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ɗaukaka Ƙara ta sauke Gwamnan Filato

Da Ɗumi-ɗumi: Kotun Ɗaukaka Ƙara ta sauke Gwamnan Filato

Daga BASHIR ISAH Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke Caleb Muftwang na PDP a matsayin halastaccen zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Filato sannan ta ayyana Dr Nentawe na Jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓe. Kotun ta yanke hukuncin ne a zaman da ta yi a wannan Lahadin. Alƙalan kotun ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a Williams-Dawodu, sun ayyana ɗan takarar Jam'iyyar APC, Dr. Nentawe Yilwatda, a matsayin halastaccen wanɗa ya lashe zaɓen. Kotun ta umarci Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), da ta janye shahadar lashe zaɓen da ta miƙa wa Mutfwang sannan ta miƙa wa Dr. Yilwatda.
Read More
Shugaban Ƙaramar Hukumar Bade ya yaba wa Buni bisa romon dimukraɗiyya da ya samar a Yobe

Shugaban Ƙaramar Hukumar Bade ya yaba wa Buni bisa romon dimukraɗiyya da ya samar a Yobe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Ƙaramar Hukumar Bade a Jihar Yobe, Alhaji Ibrahim Baba Gana, ya yaba wa Gwamna Mai Mala Buni bisa romon dimukraɗiyya da ya samar wa al'ummarsa tun daga 2019 zuwa yau, inda ya kwatanta shi da mutum mai tsananin kishin al'ummarsa da jiharsa. Honorabul Ibrahim Baba Gana ya ce Maigirma Buni ya samu nasarori wajen ciyar da Jihar Yobe gaba, inda ya ce a cikin shirye-shiryensa ya ƙarfafa wa masu ƙaramin ƙarfi da jari da kuma tallafa wa gidajen marayu, samar da ayyukan yi ga matasa masu tasowa a faɗin ƙananan hukumomin, ƙaramar hukumar…
Read More
Rashin sana’a ga matasa ne matsalar Nijeriya a yau, cewar Injiniya Abdulmutallib

Rashin sana’a ga matasa ne matsalar Nijeriya a yau, cewar Injiniya Abdulmutallib

Daga ISAH GIDAN ƁAKKO a Zariya Wani fitaccen mai sana'ar gyaran mota da ke Zariya a Jihar Kaduna mai suna Injiniya Abdulmutallib Zubairu, ya nuna matuƙar damuwarsa da yadda yara matasa ke yawo a kan tituna, ba tare da koyon wata sana'a ba. Injiniya Abdulmutallib ya nuna wannan damuwa ce jim kaɗan bayan wata jarida mai suna Taskira ta karrama shi a Zariya, kan yadda yake rungumar matasa kuma yake koya masu gyaran mota da matasan ke fitowa daga sassa daban-daban na masarautar Zazzau. Ya ci gaba da cewar, rashin samar da sana'o'in ga matasan Nijeriya musamman matasan da suke…
Read More
An tsinci gawar ’yar Nijeriya mazauniyar Birtaniya a gidanta

An tsinci gawar ’yar Nijeriya mazauniyar Birtaniya a gidanta

Daga MAHDI M. MUHAMMAD An tsinci gawar wata ’yar Nijeriya da ke zaune a Ƙasar Birtaniya mai suna Joy Nsude, a gidanta da ke Hartlepool, bayan ta gama magana da mijinta da wasu da dama ta wayar tarho. Wata 'yar Nijeriya mazauniya qasar Birtaniya, Ibironke Khadeejah Quadri ce ta bayyana rasuwar Nsude a wani sako da ta wallafa a shafin Facebook a ranar Litinin, inda ta nuna cewa ba a gano ainihin musabbabin mutuwar ta ba. Qudiri ta ce Nsude, wadda ta mutu a ranar 2 ga watan Nuwamba, ta kasance har zuwa rasuwarta, ɗalibar International Management a Jami’ar Teesside,…
Read More
Mawaƙin Hausa ya nemi BBC ta biya shi diyyar miliyan N120

Mawaƙin Hausa ya nemi BBC ta biya shi diyyar miliyan N120

Daga AISHA ASAS  Wani mawaƙin Hausa da ya ke zaune a garin Kano, Abdul Kamal, ya ɗauki matakin shari’a kan tashar BBC Hausa bisa zargin amfani da sautin waƙarshi a shahararren shirin nan nasu da ke tattaunawa da jarumai da kuma mawaƙa mai suna ‘Daga Bakin Mai Ita’. Kamar yadda Barista Bashir Ibrahim Umar, lauya mai kare wanda ke ƙarar ya bayyana, amfani da BBC ta yi da sautin waƙar mawaƙi Abdul Kamal ba tare da izininsa ba koma baya ne ga cigabansa a harkar waƙa, domin mutane za su yi tunanin shi ne ya yi satar fasaha daga sautin…
Read More
DSS ta sake gurfanar da wanda ake zargi da kai harin bom a Kano

DSS ta sake gurfanar da wanda ake zargi da kai harin bom a Kano

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar DSS a ranar Laraba a Abuja ta sake gurfanar da Husseni Ismaila, wanda aka fi sani da Maitangaran, wanda ake zargi da hannu wajen kai hare-haren bam a Kano a shekarar 2014, a babban kotun tarayya. Lokacin da aka kira lamarin, lauyan mai shigar da ƙara, Mista E.A. Aduda, ya shaida wa kotun cewa hukumar ta DSS ta shigar da ƙara ne da gyara tuhume-tuhume huɗu da ake zargin wanda ake ƙara, sannan ya roƙi kotun da ta karanta wa wanda ake ƙara laifin domin ya ɗaukaka ƙara. “Kai Husseni Ismaila, wanda ake yi wa…
Read More
El-Ghazi ya maka Mainz a kotu kan sallamarsa daga ƙungiyar

El-Ghazi ya maka Mainz a kotu kan sallamarsa daga ƙungiyar

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ɗan wasan ƙasar Holland Anwar El Ghazi na shirin ɗaukar matakin shari'a a kan tsohon ƙungiyarsa Mainz saboda korar da aka yi masa ba bisa ƙa'ida ba. Mainz ta soke kwantiragin El Ghazi a ranar 2 ga Nuwamba bayan wasu jerin rubuce-rubucen da ya yi a shafukan sada zumunta game da rikicin Isra'ila da Gaza. Mainz ta ce tawagar lauyoyin El Ghazi ne suka sanar da ita game da lamarin. A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta ƙara da cewa ba za ta ƙara yin tsokaci ba domin shari'a ce da ke gudana a halin…
Read More