Editor

9513 Posts
Neja: Gwamna Bello ya karɓi fasinjoji 39 da aka kuɓutar da su

Neja: Gwamna Bello ya karɓi fasinjoji 39 da aka kuɓutar da su

Daga FATUHU MUSTAPH Gwamnan jihar, Abubakar Sani Bello, ya karɓi mutum 53 da aka yi garkuwa da su kwanan baya a motar sufuri mallakar gwamnatin Neja (NSTA). Gwamnan ya karɓe su ne a fadar gwamnatin jihar da ke Minna, babban birnin jihar bayan da aka samu nasarar kuɓutar da su daga hannun ‘yan bindigar da suka kwashe su. Bello ya bayyana cewa, an yi nasarar kuɓutar da mutanen ne biyo bayan tattaunawa da dama da aka yi da kuma ƙwazon da gwamnati ta nuna. Yana mai cewa an kammala dukkan shirye-shirye don binciken lafiyar mutanen kafin a sada su da…
Read More
Nasarawa: Gwamna Sule ya yi ta’aziyyar rasuwar Janar Abokie

Nasarawa: Gwamna Sule ya yi ta’aziyyar rasuwar Janar Abokie

Daga BASHIR ISAH Gwamna Abadullahi A. Sule na jihar Nasarawa, ya miƙa ta'aziyyarsa ga al'ummar jiharsa, iyalai da abokan Janar Ahmed Aboki (Mai murabus) dangane da rasuwarsa. A wata sanarwa da ta sami sa hannun gwamnan, Injiniya Sule ya bayyana marigayin a matsayin ɗan'uwa wanda ya zama abin koyi a tsakanin al'umma a halin rayuwarsa. Kazalika, ya bayyana marigayin a matsayin mutumin kirki, ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa wanda ya bada gudunmuwarsa ga cigaban ƙasa. A madadin gwamnati da ma al'ummar jihar Nasarawa, Gwamna Sule ya yi ta'aziyya ga iyalai, makusanta da abokan mu'amalar marigayin bisa wannan rashi. Kana, ya…
Read More
Buhari da Lawan sun nuna alhininsu kan haɗarin jirgi a Abuja

Buhari da Lawan sun nuna alhininsu kan haɗarin jirgi a Abuja

Daga AISHA ASAS Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa kan haɗarin jirgin saman sojoji da ya auku Lahadin da ta gabata a Abuja. Sanarwar da hadimin Buhari kan sha'anin yaɗa labarai, Femi Adesina ya fitar, ta nuna yadda Shugaba Buhari ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga iyalai, 'yan'uwa da abokan aikin sojojin da suka rasu a haɗarin. Sanarwar ta ce Buhari ya bi sawun Rundunar Sojojin Sama ta Nijeriya da ma al'ummar Nijeriya baki ɗaya wajen makokin jami'an rundunar waɗanda ajalinsu ya cim musu a bakin aiki. Buhari ya ce an soma gudanar da bincike domin gano sababin haɗarin, tare…
Read More
Haɗarin jirgin sama ya ci rai 7 a Abuja

Haɗarin jirgin sama ya ci rai 7 a Abuja

Daga AISHA ASAS Wani jirgin sama mallakar Rundunar Sojin Saman Nijeriya, mai lamba NAF 201 B350, ya yi haɗari a Abuja. Bayanai sun nuna lamarin ya faru ne da hantsin Lahadi bayan da jirgin ya samu matsalar inji inda ya yi haɗari garin sauka a Abuja. Sanarwar da ta fito daga Jami'in Haulɗa da Jama'a na Rundunar, Air Commodore Ibikunle Daramola, ta nuna tuni shugaban rundunar Air Vice Marshal IO Amao, ya bada umarnin gudanar da bincike kan lamarin. Baya ga tabbatar da aukuwar lamarin, Daramola ya sake tabbatar da cewa duka mutum 7 da ke cikin jirgin sun riga…
Read More
‘Yan fashi sun cika wa ‘yan ƙungiyar Adamawa United aiki

‘Yan fashi sun cika wa ‘yan ƙungiyar Adamawa United aiki

Daga FATUHU MUSTAPHA 'Yan ƙungiyar ƙwallon ƙafa na jihar Adamawa, wato Adama United, sun gamu da wasu 'yan fashi a hanyar Benin zuwa Ore a Juma'ar da ta gabata. Bayanan da Manhaja ta kalato sun nuna 'yan fashin sun ƙwace wa 'yan wasan da jami'an ƙungiyar wasu kayayyakinsu haɗa da kuɗaɗe. 'Yan wasan suna kan hanyarsu ta zuwa Legas ne domin buga wasan da aka tsara za su buga tare da ƙungiyar MFM a nan Legas inda suka gamu da 'yan fashin da misalin ƙarfe 11:45pm. Wannan dai shi ne karo na uku da ake samu wata babbar ƙungiyoyin ƙwallon…
Read More
Ganduje ya ƙaddamar da kamfanin sarrafa abinci a kano

Ganduje ya ƙaddamar da kamfanin sarrafa abinci a kano

A Juma'ar da ta gabata Gwamnan Jihar Kano, Umar Ganduje, ya ƙaddamar da kamfanin sarrafa abinci na Mamuda Foods, a yankin rukunan masana'antu da ke Challawa. Babban Ministan Kasuwanci da Masana'antu, Hon Niyi Adebayo, da Ƙaramar Minitar Kasuwanci, Hajiya Maryam Yalwaji Katagum, su ne suka mara wa gwamnan baya wajen ƙaddamar da kamfanin.
Read More
Zaɓen ƙananan hukumomin Oyo ɓata kuɗi da lokaci ne, inji APC

Zaɓen ƙananan hukumomin Oyo ɓata kuɗi da lokaci ne, inji APC

Daga FATUHU MUSTAPHA Jam’iyyar APC a jihar Oyo, ta ce zaɓen ƙananan hukumomi da aka shirya sake gudanarwa a ranar 15 ga Mayu mai zuwa a jihar, tamkar ɓata kuɗi da kuma lokaci ne. Shugaban riƙo na APC a jihar, Chief Akin Oke, ya bayyana zaɓen a matsayin lamarin da ba zai yi armashi ba balle ya ja hankalin ‘yan siyasa na gaskiya. Yana mai cewa, an ga faruwar irin haka a baya, inda gwamnan jihar kan haifar da tsaiko ga sha’anin ƙananan hukumomin jihar waɗanda su ne mataki na uku a matakan gwamnati. Oke, ya ce zai kasance abu…
Read More
Rikicin Biliri: Gwamanati ta kafa dokar hana zirga-zirga

Rikicin Biliri: Gwamanati ta kafa dokar hana zirga-zirga

Daga WAKILIN MU Gwamnatin Jihar Gombe ta kafa dokar hana zirga-zirga na sa’o’i 24 a garin Biliri da ke cikin ƙaramar hukmar Biliri, biyo bayan rikici da ya ɓarke a yankin. Sanarwar da Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahin Abubakar Njodi, ya fitar a Juma’ar da ta gabata, ta nuna dokar ta soma aiki kai tsaye ba tare da wani jinkiri ba da zummar maido da lumana a yankin da rikicin ya shafa. “Gwamnatin jihar ta jaddada buƙatar zama da juna lafiya da kuma ƙoƙarinta wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Saboda haka gwamnati ta dakatar da haɗa kowane nau’i na…
Read More
Buhari ya yi ta’aziyya ga iyalan Dikko

Buhari ya yi ta’aziyya ga iyalan Dikko

Daga AISHA ASAS Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya miƙa taziyyarsa ga iyalai, dangi, abokan arziki, Gwamnatin Katsina da ma al’ummar jihar Katsina baki ɗaya dangane da rasuwar tsohon Shugaban Hukumar Yaƙi da Fasa-kwauri, Abdullahi Dikko Inde. Babban Hadimin Shugaban kan harkokin yaɗa labarai, Malam Garba Shehu ne ya bada sanarwar saƙon ta’aziyyar Buhari a Juma’ar da ta gabata. A cikin sanarwar, Buhari ya yaba da gudunmuwar da marigayin ya bai wa ƙasa a halin rayuwarsa, kana ya yi addu’ar Allah Ya gafarta masa kura-kuransa. Haka nan, ya yi fatan Allah ya bai wa iyalan marigayin juriya da haƙurin wannan rashi.
Read More
Ba za a biya diyya ba don kuɓutar da ɗaliban Kagara,  Minista Lai

Ba za a biya diyya ba don kuɓutar da ɗaliban Kagara, Minista Lai

Daga FATUHU MUSTAPHA Gwamnatin Tarayya ta ce babu wata diyya da za ta biya domin kuɓutar da ɗalibai da malaman sakandaren Kagara da aka yi garkuwa da su. Kazali, ta ce ba ta biya diyya ba wajen kuɓutar da ɗaliban Ƙanƙar da aka sace a jihar Katsina da kuma waɗanda aka kwashe a Dapchi, jihar Yobe. Ministan Larabarai da Raya Al’adu, Mr Lai Mohammed ne ya yi wannan bayani yayin tattaunawar da aka yi da shi a tashar talabijin ta Channels a safiyar Asabar, inda ya yi magana a kan ƙoƙarin da gwamnati ke yi wajen daƙile matsalar sace-sacen mutane…
Read More