Editor

9513 Posts
EFCC ta yi sabon shugaba

EFCC ta yi sabon shugaba

Daga AISHA ASAS Majalisar Dattawan Nijeriya ta tabbatar da Abdulrasheed Bawa a matsayin sabon Shugaban Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Zagon Ƙasa da Zambar Kuɗaɗe (EFCC). Sanatocin sun shafe sa'o'i biyu suna tantance Bawa kafin daga bisani suka tabbatar da shi a sabon matsayin nasa. Yayin da ake tantance shi, Bawa ya bai wa majalisar tabbacin cewa zai yi aiki tukuru don gyara wa hukumar zama ta hanyar inganta harkokinta kafin ƙarewar wa'adin jagorancinsa. Bawa ya ce zai yi aiki tare da waɗanda suka dace a sassan duniya domin tabbatar da Nijeriya ta amfana da dukiyoyinta da aka…
Read More
Makinde ya sake buɗe kasuwar Shasha

Makinde ya sake buɗe kasuwar Shasha

Daga AISHA ASAS Bayan shafe kimanin makonni biyu da rufe kasuwar Shasha a jihar Oyo sakamakon ɓarkewar rikici a tsakanin 'yan kasuwan kasuwar, Gwamna Seyi Makinde ya bada umarnin sake buɗe kasuwar ba tare da wani jinkiri ba. Makinde ya buƙaci sake buɗe kasuwar ne yayin wata ganawa da ya yi da shugabannin Hausawa da Yarabawan yankin a fadar gwamnatin jihar da ke Ibadan. Gwamnan ya ce an ɗauki matakin sake buɗe kasuwar ne duba da yadda rufe kasuwar ya yi tasiri kan tattalin arzikin yankin da ma jihar baki ɗaya. Ya ce yayin da ya ziyarci Sarkin Sasa da…
Read More
An yi garkuwa da sirikar Mangal a Katsina

An yi garkuwa da sirikar Mangal a Katsina

Daga FATUHU MUSTAPHA Rahotannin da Manhaja ta samu daga jihar Katsina, sun nuna 'yan bindiga sun sace sirikar hamshaƙin ɗan kasuwar nan Alhaji Dahiru Barau Mangal, a Katsina. Majiyar Manhaja ta ce lamarin ya faru ne a daren Talata a yankin ƙaramar hukumar Matazu, inda 'yan bindigar suka je suka ɗauki Hajiya Rabi. Majiyar wadda ta buƙaci a sakaya sunanta, ta ce da misalin karfe 1 na daren Talata 'yan bindigar suka shiga gari suka tafi kai tsaye zuwa gidan Hajiya Rabi suka ɗauke ta suka yi gaba ba tare da an san inda suka nufa ba. Da ma dai…
Read More
EFCC ta kama ‘yan fashin intanet 9 a Minna

EFCC ta kama ‘yan fashin intanet 9 a Minna

Daga BASHIR ISAH Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Zagon Ƙasa da Zambar Kuɗaɗe (EFCC), ta cafke wasu 'yan fashin intanet su tara a Minna, babban birnin jihar Neja. EFCC ta cafke waɗanda lamarin ya shafa ne a ranar Litinin biyo bayan bayanan sirri da ta ce ta samu a kansu dangane da ayyukan zambatar mutane da suke aikatawa. Kayayyakin da EFCC ta ce ta ƙwace a hannu matasan sun haɗa da ƙananan kwamfutoci da wayoyin salula da kuma motoci. Hukumar ta ce, za ta gurfanar da 'yan fashin a kotu da zarar ta kammala bincikenta.
Read More
Ortom ya nemi Bala ya bai wa ‘yan ƙasa haƙuri kan furucinsa

Ortom ya nemi Bala ya bai wa ‘yan ƙasa haƙuri kan furucinsa

Daga AISHA ASAS Gwamnan Jihar Binuwai, Samuel Ortom, ya buƙaci takwararnsa na jihar Bauchi, Bala Mohammed, da ya fito ya bai wa 'yan Nijeriya haƙuri game da furucin da ya yi na goyon bayan Fulani makiyaya su riƙa amfani da bindiga wajen kare kansu. Ortom ya buƙaci haka ne yayin taron manema labarai da ya gudana a Makurdi a Litinin da ta gabata inda ya ce akwai buƙatar Gwamna Bala ya bada haƙuri domin sanyaya zukatan waɗanda suka rasa 'yan'uwa sakamakon ayyukan ɓatagarin Fulani makiyaya. Kazalika, Ortom ya buƙaci Gwamna Bala da ya yi koyi da takwarorinsa na Kano da…
Read More
Gwamnati ta buƙaci gidajen talabijin su riƙa fassara labarunsu da yaren kurame

Gwamnati ta buƙaci gidajen talabijin su riƙa fassara labarunsu da yaren kurame

Daga FATUHU MUSTAPHA Gwamnatin Tarayya ta bada umurnin tashoshin talabijin a faɗin ƙasa su riƙa amfani da yaren kurame a lokutan gabatar da labarai don fassara labarun da suke bayarwa don ƙaruwar masu fama da nakasa. Ministan Labarai da Al'adu, Lai Mohammed ne ya bada wannan umurni yayin wani taro da suka gudanar ta bidiyo tare da jami'an Cibiyar Kula da Nakasassu, a Litinin da ta gabata a Abuja. Wannan na zuwa ne bayan da shugaban cibiyar nakasassun, David Anyaele, ya yi ƙorafin an baro masu fama da nakasa a baya game da sha'anin labarun da tashoshin kan bayar balle…
Read More
Ministar Jinƙai ta jajanta kan faɗowar jirgin saman sojoji

Ministar Jinƙai ta jajanta kan faɗowar jirgin saman sojoji

Daga WAKILIN MU Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta bayyana alhinin ta kan faɗowar jirgin saman Rundunar Mayaƙan Sama ta Nijeriya (NAF) ƙirar Beechcraft KingAir B350i Aircraft a ranar Lahadi a Abuja. Rahotanni sun ce jirgin ya samu matsalar inji bayan ya tashi sannan ya faɗo ƙasa. Hajiya Sadiya ta bayyana baƙin ciki kan haɗarin jirgin da kuma asarar rayukan waɗanda ke cikin jirgin da aka yi. Ta ce, "Ina cikin tsananin alhini da baƙin cikin wannan abu maras daɗi da ya faru. Ina miƙa gaisuwa ta ga Rundunar Mayaƙan Sama da iyalan waɗanda…
Read More
IMO: An buƙaci Buhari da shugabannin APC su shiga tsakanin Uzodima da Okorocha

IMO: An buƙaci Buhari da shugabannin APC su shiga tsakanin Uzodima da Okorocha

Daga AISHA ASAS Wani gungun magoya bayan dimukraɗiyya sun gudanar da zanga-zangar lumana a Abuja inda suka nuna rashin jin daɗinsu dangane da kama tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okoroca, da 'yan sanda suka yi tare da yin kira ga Shugaba Buhari da sauran shugabannin APC a kan su gaggauta shiga tsakani. An ga masu zanga-zangar ɗauke da kwalaye waɗanda aka rubuta saƙonni daban-daban a jikinsu masu nuna rashin kyautatuwar abin da Gwamnan Imo, Hope Uzodima ya yi da kuma nuna goyon baya ga Rochas. Masu zanga-zangar sun ra'ayin cewa kama Okorocha da aka yi take-take ne na neman…
Read More
Bayan shekara 10, New Zealand na jimamin girgizar ƙasar da ta fuskanta

Bayan shekara 10, New Zealand na jimamin girgizar ƙasar da ta fuskanta

Daga WAKILIN MU A wannan Litinin ne Ƙasar New Zealand ke cika sheka 10 da faruwar ibtila'in girgizar ƙasa da ya auku a birnin Christchurch wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 185, tare da jikkata wasu dubbai. Girgizar ƙasar wadda ta kai ƙarfin maki 6.3 da zurfin kilomita 5, ta faru ne a ranar 22, Fabrairu, 2011. Domin tuna zagayowar wannan rana, ɗaruruwan 'yan ƙasar ne suka taru a wani wajen taro a birnin Christchurch domin tunawa da duka waɗanda suka rasa rayukansu a wancan lokaci. Haka nan, an ga yadda aka yi ƙasa-ƙasa da tutoci a sassan ƙasar domin…
Read More