26
Feb
Daga FATUHU MUSTAPHA Rahotanni daga Jihar Zamfara, sun nuna cewa 'yan bindiga sun sace ɗalibai mata kusan su 300 a Makarantar Sakandaren Gwamnati (GSS) Jangeɓe, da ke yankin ƙaramar hukumar Talata-Mafara a jihar, a tsakar daren Juma'a. Kwamishinan Labarai na jihar, Malam Suleiman Tunau Anka, ya tabbatar wa manema labarai faruwar haka, inda ya ce 'yan bindiga sun shiga makatar ne da misalin ƙarfe 1 na tsakar daren Juma'a suka kwashi ɗalibai. Sai dai Anka bai faɗi adadin ɗaliban da lamarin ya shafa ba. Wannan na faruwa a daidai lokacin da Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle, ya yi kira ga…
