Editor

9513 Posts
Minista Dare ya ƙaddamar da gasar ‘Principal Cup’

Minista Dare ya ƙaddamar da gasar ‘Principal Cup’

Daga BASHIR ISAH An ƙaddamar da gasar ƙwallon ƙafa na 'Principal Cup'. Ministan Matasa da Wasannin Motsa Jiki, Mr Sunday Dare ne ya ƙaddamar da gasar a birnin Legas a wannan Juma'a. Bayan ƙaddamar da gasar, Igbobi da kuma Government College Kaduna, su ne suka fara fafatawa a filin wasannin motsa mitsa jiki na Agege, Legas. A cewar Minista Dare wanda shi ne silar farfaɗo da gasar 'Principal Cup', " Cikar buri ne kuma abin farin ciki ganin wannan gasa ta kankama a yau. "Muna alfahari da wasan da waɗannan matasa suka yi a yau. Ina fata wannan zai zama…
Read More
Yadda na samu kaina a harkar fim, Saratu Giɗaɗo (Daso)

Yadda na samu kaina a harkar fim, Saratu Giɗaɗo (Daso)

Fitacciyar jaruma a masana’antar shirya finafinai ta Kannywood, Saratu Giɗaɗo wadda aka fi sani da sunan Daso, jaruma ce da ta daɗe ana damawa da ita a cikin masana’antar, wadda a yanzu idan ana maganar dattawan cikin harkar fim to Saratu za ta iya shigowa cikin su.Tsawon shekarun da ta shafe a matsayin ba tare da an daina yayin ta ba ya kai ta ga zama kaɗan daga cikin jaruman da su ka kafa tarihi a cikin masana’antar domin wasu ɗan lokaci kaɗan su ke ci sai a daina ganin su, ko dai a ce sun bar harkar, ko kuma…
Read More
Ba a koyon rubutu, ba a sayen sa da kuɗi – Jamila Rijiyar Lemu

Ba a koyon rubutu, ba a sayen sa da kuɗi – Jamila Rijiyar Lemu

Jamila Abdullahi Rijiyar Lemu ƙwararriyar marubuciya ce da ta daɗe tana jan zaren ta a duniyar rubuta littattafan Hausa.  Kuma ta yi zarrar zuwa ta biyu a gasar da sashen Hausa na BBC ke shirya wa mata zalla a duk shekara, wato ‘Hikayata,’ a shekarar 2019. A wannan tattaunawar da wakiliyar Manhaja, za ku ji yadda marubuciyar ta sha gwagwarmaya da faɗi-tashi a harkar rubutu. Daga AISHA ASS Mu fara da jin tarihin ki a taƙaice.Bismillahir Rahmanir Rahim! Suna na Jamila Abdullahi Rijiyar Lemu. An haife ni a shekara ta 1980. Na yi karatu tun daga firamare zuwa Jami’ar Bayero…
Read More
Tallafin naira biliyan 600 ga manoma

Tallafin naira biliyan 600 ga manoma

Labarin da aka bayar cewa Gwamnatin Tarayya na shirin bada tallafin sama da naira biliyan 600 don agaza wa manoma abin farin ciki ne. Ba shakka, abin da ya dace ne idan har ana so a faɗaɗa hanyoyin inganta tattalin arzikin ƙasar nan, wanda ya shafe sama da shekara hamsin ya na dogaro da man fetur wajen samun kuɗaɗen shiga. Ministan Aikin Gona Da Raya Yankunan Karkara, Alhaji Sabo Nanono, shi ne ya bayyana labarin a cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na ma’aikatar sa, Mista Theodore Ogaziechi, ya rattaba wa hannu kwanan nan a Abuja. A sanarwar, an…
Read More

Zawiyyoyi da gudunmawar su wajen ilmantarwa da inganta rayuwar al’umma

Daga Tahir Lawan Muaz Attijaneey Gabatarwa: Da sunan Allah, mai rahama mai jinƙai, tsaira da amincin Allah su tabbata ga Shugaban Talikai Sayyadina Rasulillahi ɗan Abdullahi da Aminatu, tare da Ahlin gidansa tsarkaka da Sahabbansa baki ɗaya. Bayan haka, wannan maudu’i da aka ba ni na yi bayani a kansa ƙarƙashin wannan mu’asasah ta AL-SUFF FOUNDATION yana da matukar faɗi, hasali ma idan muka ɗauke shi gaɓa gaɓa za muga ya ƙunshi ɓangarori biyu manya wato bayani kan zawiya sai kuma gudunmawarsu wajen ilmantarwa da inganta rayuwa. Har ila yau, idan muka koma za mu ga cewa shin ana so…
Read More
Ɗanwaire gwanki sha bara (1924)

Ɗanwaire gwanki sha bara (1924)

Daga FATUHU MUSTAPHA Babu takamaiman ko wacce shekara aka haifi Ɗanwaire, sai dai an bayyana cewa asalin sunan sa Muhammadu. Iyayen sa da alama dai Fulani ne, kuma asalain sa shi da mutumin Kano ne. an haife shi a garin Waire da ke ƙasar Bichi a yanzu. Babu kuma wani cikakken bayani akan ko wane irin nau’in Fulani ne. A taƙaice dai, asali da tasowar Ɗanwaire abu ne da har yau masana basu samu wani cikakken bayani a ka ba. Amma dai an fara jin ɗuriyar Ɗanwaire ne a zamanin sarkin Kano Bello1882 – 1893. Hakan na nuni da cewa…
Read More
An daina kishi na faɗan baki, sai na ƙwandala – Khadija Mahuta

An daina kishi na faɗan baki, sai na ƙwandala – Khadija Mahuta

Hajiya Khadija Abdulrasheed Mahuta mace ce wadda ya kamata mata su yi koyi da ita, kasancewar ta jaruma kuma tsayayya, sannan da ta san ciwon kan ta. Ta kasance cikin jerin mata da su ke tauna taura biyu a lokaci guda. Ma’ana, mace ce wadda ba ta zauna ba don jiran sai wani ya samo ya kawo mata, a’a, ta tashi tsaye ne haiƙan wajen rufa wa kan ta asiri. Wakiliyar Manhaja ta tattauna da ita inda ta bayyana wa masu karatu rayuwar ta wadda za ta iya zama makaranta ga mata. Daga AISHA ASAS Masu karatu za su so…
Read More
Za mu yi maganin ‘yan fashi da masu tada ƙayar-baya, cewar Buhari

Za mu yi maganin ‘yan fashi da masu tada ƙayar-baya, cewar Buhari

Daga FATUHU MUSTAPHA Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, yayi gargaɗin cewa babu wani sassauci game da matakan da gwamnati ta shirya ɗauka na neman kawar da matsalolin 'yan fashi da masu tada ƙayar-baya da sauran manyan laifuka da suka addabi al'umma a faɗin ƙasa. Buhari ya yi wannan gargaɗi ne ta bakin Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Farfesa Ibrahim Gambari, yayin wani taro kan sha'anin tsaro wanda gwamnonin Arewa da sarakunan gargajiya suka gudanar a Jihar Kaduna. Buhari ya yarda cewa lallai Nijeriya na fama da matsalolin tsaro, amma cewa ya buƙaci sabbin shugabannin tsaro da samar da sabbin dabaru kuma…
Read More
Legas: Hukumar Kwastam ta kama taramo katan 554

Legas: Hukumar Kwastam ta kama taramo katan 554

Daga AISHA ASAS Ofishin Hukumar Yaƙi da Fasa-ƙwauri ta Nijeriya (NCS) da ke Apapa a Legas, ya ce ya kama wani kwantena mai lamba 1793504 wanda aka yi amannar tais (tiles) ne aka ɗauko, amma bayan da aka zurfafa bincike sai aka gano katan-katan na ƙwayar taramo guda 554 maƙare a cikin sunduƙin. Da yake yi wa manema labarai bayani a ranar Alhamis da ta gabata Shugaban Hukumar na Apapa, Controller Malanta Yusuf, ya ce kimanin makonni uku da kama aiki a Apapa, sun yi nasarar kama sunduƙai da dama ɗauke da kayayyakin da aka haramta shigo da su cikin…
Read More
Bauchi: Za a kammala sansanin alhazai kafin Hajjin bana

Bauchi: Za a kammala sansanin alhazai kafin Hajjin bana

Daga WAKILIN MU Gwamnatin Jihar Bauchi ta bada tabbacin cewa, za ta kammala aikin gina katafaren sansanin alhazai na ƙasa-da-ƙasa da ta sa a gaba kafin aikin Hajjin 2021 ya kankama. Sakataren Hukumar Kula da Jin Daɗin Alhazai na jihar, Alhaji Abubakar Babangida Tafida (Tafidan Giade), shi ne ya bada wannan tabbaci yayin ziyayar da ya kai a sansanin a ranar Alhamis da ta gabata don gane wa idanunsa yadda aiki ke gudana. Jim kaɗan bayan kammala ziyarar, Babangida Tafida ya shaida wa manema labarai cewa, aikin sansanin alhazan na ɗaya daga cikin ƙudurorin gwamnatin Gwamna Bala Abdulkadir Muhammad na…
Read More