Shugaban Ƙaramar Hukumar Bade ya yaba wa Buni bisa romon dimukraɗiyya da ya samar a Yobe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Ƙaramar Hukumar Bade a Jihar Yobe, Alhaji Ibrahim Baba Gana, ya yaba wa Gwamna Mai Mala Buni bisa romon dimukraɗiyya da ya samar wa al’ummarsa tun daga 2019 zuwa yau, inda ya kwatanta shi da mutum mai tsananin kishin al’ummarsa da jiharsa.

Honorabul Ibrahim Baba Gana ya ce Maigirma Buni ya samu nasarori wajen ciyar da Jihar Yobe gaba, inda ya ce a cikin shirye-shiryensa ya ƙarfafa wa masu ƙaramin ƙarfi da jari da kuma tallafa wa gidajen marayu, samar da ayyukan yi ga matasa masu tasowa a faɗin ƙananan hukumomin, ƙaramar hukumar Bade da suka haɗa da samar da ingantattun cibiyoyin kiwon lafiya a cikin birane da ƙauyuka a cikin ƙaramar hukumar Bade da sauran ƙananan hukumomi 17 na jihar.

Hakazalika ya ce Buni ya samar da ingantaccen ilimi a matakin firamare da sakandire tare da samar da kujeru da tebura.

Haka kuma ya samar da ƙwararrun malamai masu digiri da NCE domin yara su samu ilimi mai inganci.

Ya ce : “Maigirma Gwamna ya samar da ingantaccen ruwa da a cikin gari da ƙauyaku ta hanyar gyare-gyare da kula da rijiyoyin burtsatse a dukkan gundumomi da ƙauyukan ƙaramar hukumar Bade.

“Ya sayo motoci ga jami’an tsaro da na’urori don tabbatar da an kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da ganawa akai-akai da shugabannin qananan hukumomi, jami’an tsaro, dagatai da sauran masu ruwa da tsaki a ƙaramar hukumar Bade.

Game da Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Gabas NEDC, Honorabul Ibrahim Baba Gana ya ce sun yi maraba da farin cikin kafa hukumar da tsohon shugaban ƙasa Muhammad Buhari da tsohon shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan.

Da ƙarshe Baba Gana ya ja hankalin matasan ƙaramar hukumar Bade a kodayaushe, ya kamata su mutunta kundin tsarin mulki sannan kuma su mutunta dattijai a cikin al’ummarsu kasancewar su ne shugabannin gobe.

Shugaban Ƙaramar Hukumar na Bade ya kuma jinjina wa tsohon Shugaban Majalisar Dattawa ta tara, Sanata Ahmed Lawan, bisa yadda ya samar wa matasa maza da mata daga mazaɓarsa ayyukan yi a matakin Gwammatin Tarayya da jiha.

Ya bayyana cewa al’ummar Jihar Yobe da Nijeriya bakiɗaya ba za su taɓa mantawa da gudunmuwar da ya bai wa yankinsa da ƙasar ba.