Rashin sana’a ga matasa ne matsalar Nijeriya a yau, cewar Injiniya Abdulmutallib

Daga ISAH GIDAN ƁAKKO a Zariya

Wani fitaccen mai sana’ar gyaran mota da ke Zariya a Jihar Kaduna mai suna Injiniya Abdulmutallib Zubairu, ya nuna matuƙar damuwarsa da yadda yara matasa ke yawo a kan tituna, ba tare da koyon wata sana’a ba.

Injiniya Abdulmutallib ya nuna wannan damuwa ce jim kaɗan bayan wata jarida mai suna Taskira ta karrama shi a Zariya, kan yadda yake rungumar matasa kuma yake koya masu gyaran mota da matasan ke fitowa daga sassa daban-daban na masarautar Zazzau.

Ya ci gaba da cewar, rashin samar da sana’o’in ga matasan Nijeriya musamman matasan da suke Arewa wannan a cewarsa shi ya haifar da matsalolin tsaro da ya addabi kowa musamman a Arewacin Nijeriya.

A nan ne Injiniya Abulmutallalib ya shawarci duk wanda yake da sana’ar hannu ya fara tunanin makomar matasan Nijeriya a zuciyarsa.

Ya ƙara da cewar rashin sa ido ga yara su samu sana’ar da zai tallafa wa rayuwarsu na kan gaba, na matsalolin da suka zama silar ƙamfar tsaro a Arewa za su zama tarihi a ɗan lokaci kaɗan.

Injiniya Zubairu ya tabbatar da cewar matuƙar aka ƙara sa ido na ganin yara sun samu sana’ar da za su rayu har su tallafa wa wasu matsalolin tsaro a Arewa za su zama tarihi a lokaci kaɗan.

Da kuma Injiniya Abdulmutallib Zubairu ke tsokaci kan karramawar da aka yi masa, ya ce an qara masa ƙwarin gwiwar ƙara tashi tsaye wajen koyar da matasa wannan sana’a ta gyaran mota.