An tsinci gawar ’yar Nijeriya mazauniyar Birtaniya a gidanta

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

An tsinci gawar wata ’yar Nijeriya da ke zaune a Ƙasar Birtaniya mai suna Joy Nsude, a gidanta da ke Hartlepool, bayan ta gama magana da mijinta da wasu da dama ta wayar tarho.

Wata ‘yar Nijeriya mazauniya qasar Birtaniya, Ibironke Khadeejah Quadri ce ta bayyana rasuwar Nsude a wani sako da ta wallafa a shafin Facebook a ranar Litinin, inda ta nuna cewa ba a gano ainihin musabbabin mutuwar ta ba.

Qudiri ta ce Nsude, wadda ta mutu a ranar 2 ga watan Nuwamba, ta kasance har zuwa rasuwarta, ɗalibar International Management a Jami’ar Teesside, Middlesbrough.

Ta kuma ce Nsude uwa ce mai ’ya’ya biyu, yaro ɗan shekara 4 da yarinya ’yar shekara biyu.
A wani labarin kuma, rundunar ’yan sandan Jihar Ekiti ta sanar da bacewar wani mutum mai suna Joseph Anifowose mai shekaru 30 da haihuwa.

Hakan na qunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, DSP Abutu Sunday, ya sanyawa hannu a ranar Talata a Ado-Ekiti.

Ya ce, Anifowose na Lane 6, Wonder City College, Ado-Ekiti, ya bar gida ne a ranar 6 ga watan Nuwamba, da misalin ƙarfe 08:00 na safe zuwa wata cibiyar kallon ƙwallon ƙafa, bai dawo ba.

Sunday ya ce shi duhu ne a fuskarsa, tsayinsa ƙafa shida, yana jin harsunan Yarbanci da Ingilishi sosai kuma ba shi da alamar ƙabila.

Rundunar ta ce, ta fara bincike domin gano inda yake.