Mawaƙin Hausa ya nemi BBC ta biya shi diyyar miliyan N120

Daga AISHA ASAS 

Wani mawaƙin Hausa da ya ke zaune a garin Kano, Abdul Kamal, ya ɗauki matakin shari’a kan tashar BBC Hausa bisa zargin amfani da sautin waƙarshi a shahararren shirin nan nasu da ke tattaunawa da jarumai da kuma mawaƙa mai suna ‘Daga Bakin Mai Ita’.

Kamar yadda Barista Bashir Ibrahim Umar, lauya mai kare wanda ke ƙarar ya bayyana, amfani da BBC ta yi da sautin waƙar mawaƙi Abdul Kamal ba tare da izininsa ba koma baya ne ga cigabansa a harkar waƙa, domin mutane za su yi tunanin shi ne ya yi satar fasaha daga sautin shirin nasu don neman suna.

“Muna kira ga kotu da ta tursasa wa BBC biyan Naira miliyan 120 a matsayin dameji, kuma kotu ta tilasta wa BBC tsayar da amfani da waqar har sai an cimma matsaya,” inji Barista Bashir. 

Yayin mayar da martani, lauyan BBC, Shakirudden Mosobalage, ya sheda wa kotu cewa, BBC ta siye sautin ne daga wani kamfani da ke birnin tarayya, Abuja.

Sannan ya nemi kotu ta ba shi lokaci don ya tattaro takardu da zai gabatar wa kotu a matsayin hujja. Kuma kotu ta amince da hakan.

Kutun ƙarƙashin jagorancin Justice N.M. Inusa, ta ɗage sauraron ƙarar har zuwa watan gobe, 12 ga watan Disamba, 2023.