Editor

9276 Posts
Zaɓen Bayelsa, Imo, Kogi: Ban da nuna halin a-yi-rai-ko-a-mutu, kiran Kwamitin Abdulsalami ga ‘yan siyasa

Zaɓen Bayelsa, Imo, Kogi: Ban da nuna halin a-yi-rai-ko-a-mutu, kiran Kwamitin Abdulsalami ga ‘yan siyasa

Daga BASHIR ISAH Shugaban Kwamitin Wanzar da Zaman Lafiya na Ƙasa, Janar Abubakar Abdulsalami (rtd), ya yi kira ga jam'yyun siyasa da magoya bayansu da a guji nuna halin a-yi-rai-ko-a-mutu yayin zaɓen gwamnonin da za a gudanar ranar Asabar a jihohin Bayelsa da Kogi da kuma Imo. Abdulsalami ya yi wannan kira ne yayin da jam'iyyin siyasa su 18 da za su fafata a zaɓen gwamna a Jihar Kogi suka rattaɓa hannun kan yarjejeniyar zaman lafiya ranar Laraba a jihar. Da yake jawabi ta bakin wakilinsa Cardinal John Onaiyekan, tsohon shugaban ƙasar ya ce: “Wannan taro na da muhimmanci saboda…
Read More
Ƙungiyar Marubuta ta Ƙasa reshen Jihar Kano ta yi sabbin shugabanni

Ƙungiyar Marubuta ta Ƙasa reshen Jihar Kano ta yi sabbin shugabanni

Daga IBRAHIM HAMISU, Kano Ƙungiyar marubuta ta ƙasa reshen Jihar Kano, wato Association of Nigerian Authors (ANA) ta yi sabbin shugabanni da ya biyo bayan taron da ya gudana a ɗakin karatu na Murtala Muhammed ranar Lahadi da ta gabata. An dai yi zaɓen ƙungiyar ne yayin gabatar da manyan taruka da ta saba gudanarwa duk ƙarshen wata. An kuma zavi Dr.Murtala M. Uba wanda malami ne a sashen ilimin nazarin ƙasa wato (Geography) da ke jami'ar Bayero Kano a matsayin sabon shugaban ƙungiyar. Jim kaɗan bayan kammala zaɓen ne dai, sabon shugaban Dr. Murtala Uba ya ce, za su…
Read More
Kowa ya yi rubutu mai kyau zai samu karɓuwa – Ado Ahmad MON

Kowa ya yi rubutu mai kyau zai samu karɓuwa – Ado Ahmad MON

"Kyakkyawar mu'amala da mutane tasa ake karrama ni" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Sunan Ado Ahmad Gidan Dabino (MON) Sani Mai Nagge, ba ɓoyayye ba ne a duk faɗin ƙasar nan, ba ma tsakanin marubuta da masu shirya finafinai ba, har ma da manazarta na ƙasa da ƙasa. Ya yi rubuce-rubuce da dama cikin harsunan Hausa da Turanci, a ciki har da littafin da yanzu haka ya shiga cikin manhajar koyar da Hausa a manyan makarantun sakandire na qasar nan. Ya samu shaidar karramawa iri-iri da suka jawo masa ɗaukaka a duniya fiye da duk wani marubucin Hausa. A zantawarsa da…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: Kotu ta bada belin Emefiele

Da Ɗumi-ɗumi: Kotu ta bada belin Emefiele

Daga BASHIR ISAH Babbar Kotun Tarayya mai zamanta a Abuja ta bada belin tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele. Kotu ta bada belin yayin zaman da ta yi a ranar Laraba domin sauraren ƙarar neman beli da Emefiele ya shigar. Mai Shari'a Olukayode Adeniyi ne ya bada belin tare da miƙa Emefiele ga lauyoyinsa inda ake sa ran su gabatar da shi a Babbar Kotun Abuja a ranar 15 ga Nuwamba kotun da a nan ne EFCC ta shigar da ƙara a kan Emefiele da wani. Lauyoyin da kotun ta miƙa wa Emefiele su ne Matthew Burkaa (SAN)…
Read More
Bayan tsaftace ƙasa daga fasadi sai a waiwayi yunwa

Bayan tsaftace ƙasa daga fasadi sai a waiwayi yunwa

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU A lokacin da nake wannan rubutun, jami'an Hukumar Hisba ta Jihar Kano na can na aikin tantance matasan da jami'anta suka kama bisa laifin aikata fasadi, yawon dare, da mu'amala a wuraren da suke ɓata tarbiyyar al’umma, biyo bayan samame da suke kai wa a wasu gidajen karuwai, kulob-kulob, da ɓoyayyun wuraren da ɓatagari ke fakewa suna aikata ɓarna cikin dare a sassa daban-daban na cikin birnin Kano. Sannan a wata tattaunawa da tashar rediyon Freedom ta yi da wasu daga cikin waɗannan matasa sun bayyana wuraren da aka kama su, da abubuwan da suka ce…
Read More
Asara ce mace ta riƙe wayar N50,000 ba ta kawo mata N5,000 – Ayat Adamu 

Asara ce mace ta riƙe wayar N50,000 ba ta kawo mata N5,000 – Ayat Adamu 

"Idan ka ji shiru a gidan aure, ba ƙorafi, matar na sana'a" Daga AISHA ASAS  (Ci gaba daga makon jiya) Mai karatu barkanmu da sake ganin zagayowar sati lafiya. Idan ba ku shafa'a ba, a satin da ya gabata, mun ɗauko tattaunawa da fitacciyar 'yar kasuwa mai kishin matan Arewa, Ayat Uba Adamu. Inda muka soma da jin tarihin rayuwarta, zuwa irin sana'ar da take yi, kafin mu tsunduma kan yadda take gudanar da kasuwancin nata. A tattaunawar, Hajiyar ta sheda wa Manhaja irin yunƙurin da ta yi na kafa ƙungiya musamman domin mata masu kasuwanci da ke tu'ammali da…
Read More
Zaɓuɓɓukan 11 ga Nuwamba: Za mu yi watsi da ƙuri’un duk rumfar zaɓen da aka samu hayaniya – INEC

Zaɓuɓɓukan 11 ga Nuwamba: Za mu yi watsi da ƙuri’un duk rumfar zaɓen da aka samu hayaniya – INEC

Daga BASHIR ISAH Yayin da rage 'yan kwanaki ƙalilan kafin zaɓen gwamna a wasu jihohin Nijeriya, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta yi gargaɗin ba za ta kula ƙuri'un duk wata rumfar zaɓe da aka fuskanci tashin-tashina ba. Shugaban INEC, Mahmood Yakubu ne ya yi wannan gargaɗi yayin taron masu ruwa da tsaki da ya gudanar ranar Talata a Yenagoa, babban jihar Bayelsa. Ya zuwa ranar 11 ga Nuwamban da ake ciki ne ake sa ran INEC za ta gudanar da zaɓen gwamnoni a jihohin Bayelsa, Kogi da kuma Imo. Yakubu, wanda ya samu wakilcin Kwamishinan INEC mai lura yankunan…
Read More
Zuwa ga mata: Bayan rabuwar aure (2)

Zuwa ga mata: Bayan rabuwar aure (2)

Tare da AMINA YUSUF ALI Barkanmu da sake haɗuwa a wani makon. Sannunku da jimirin karatun filinku na Zamantakewa a jaridar Manhajarku mai farin jini. A makon da ya gabata na yi magana a kan zawarawa da barazanar da suke fuskanta. Yanzu za mu ɗora daga inda aka tsaya a wancan mako. A sha karatu lafiya. Yanzu za mu daga inda muka tsaya a cikin jerin dalilan da wasu zawarawan suke kauce hanya. Ko na ce suke yin ayyuka na rashi kamun kai. *Rashin haƙuri: Wasu matan da ma Allah ya halicce su da ɗabi'ar rashin haƙurin iya zama ba…
Read More
Tinubu ya miƙa saƙon ta’aziyya kan rasuwar Sheikh Yusuf Ali

Tinubu ya miƙa saƙon ta’aziyya kan rasuwar Sheikh Yusuf Ali

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhininsa kan rasuwar babban malamin addinin Musulunci, Sheikh Yusuf Ali, wanda ya rasu a safiyar ranar Litinin, yana da shekaru 73 a duniya. Shugaban ya aike da saƙon alhini zuwa ga iyalai, ɗalibai, da kuma mabiya wannan malami da ke Kano, da ma Masarautar Gaya wanda wannan malami ke kan karagar Sarkin Malamanta a lokacin rayuwarsa. Tinubu ya miƙa saƙon ta'aziyyar ne ta hannun mai magana da yawunsa, wato Ajuri Ngelale. Ya bayyana rasuwar jagoran addinin a matsayin wani babban abun alhinin da ya karaɗe muryoyin jama'a a faɗin ƙasar nan, duba da irin…
Read More
An kammala ɗaukar shirin fim ɗin ‘Princess Of Galma’

An kammala ɗaukar shirin fim ɗin ‘Princess Of Galma’

DAGA MUKHTAR YAKUBU A ƙarshen satin da ya gabata ne aka kammala ɗaukar shirin fim na Turanci mai suna 'Princess Of Galma' wanda aka shafe tsawon kwanaki 12 ana gudanar da shi. Shirin wanda kamfanin da ya saba shirya finafinan Turanci a Kannywood na Jammaje Productions ya ɗauki nauyin shirya shi kuma aka yi aikin sa a cikin garin Kano a wannan lokacin, kuma ƙwararren darakta Galadima Muhammad ne ya bayar da umarni yayin da jarumai irin su Magaji Mijinyawa na 'Gidan Badamasi', Ishak Sidi Ishak, Hajara Makama, Faruk Sayyadi, Mustapha Musty, Zainab Bichi, Aisha A Musa, da sauran jarumai…
Read More