12
Mar
Daga FATUHU MUSTAPHA Ƙungiyar 'Yan Kasuwar Fetur Masu Zaman Kansu ta Nijeriya (IPMAN), ta ce ba ta samu wata sanarwar ƙarin kuɗin fetur a hukumance ba, don haka ta buƙaci mambobinta da su yi watsi da jita-jitar da ake ta yaɗawa game da ƙarin farashin fetur. A wata ganawa da ya yi da manema labarai a wannan Juma'ar, shugaban IPMAN reshen jihar Kano, Bashir Dan-Malam, ya bai wa mambobinsu umarnin su ci gaba da saida fetur kan farashin N163 kowace lita. Yana mai cewa duk lokacin da aka samu ƙarin farashin mai a ƙasa, masu ruwa da tsaki na fannin…
