10
Mar
10
Mar
Daga UMAR M. GOMBE Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta bada sammaci wanda ya tilasta wa Babban Lauyan Tarayya (AGF), Abubakar Malami SAN, da tsohon shugaban riƙo na hukumar EFCC Ibrahim Magu, da su bayyana a gabanta. Kotu ta buƙaci ganin waɗanda lamarin ya shafa ne domin su bada shaida a shari’ar cin hanci da rashawa da ake yi wa tsohon shugaban kwamitin gyaran fansho, Abdulrasheed Maina. Kazalika, kotun ta umarci Shugaban Babban Bankin Ƙasa (CBN), Godwin Emefiele da wasu da su bayyana a gabanta a ranakun 9, 10 da 11 na Maris domin bada shaida. Sauran mutanen da…
10
Mar
Daga AISHA ASAS Gwamnatin Tarayya ta ce ba ta yarda 'yan kasuwa su shigo da allurar rigakafin cutar korona ba, tare da cewa dole dukkan rigakafin da za a shigo da su ya kasance ta hannun gwamnati. Ƙaramin Ministan Lafiya, Olorunnimbe Mamora ya faɗi haka ran Talata a Abuja.Ministan ya ce 'yan Nijeriya masu bukatar a yi musu rigakafin korona sai su yi rajista a shafin intanet na Hukumar Kula da Lafiaya a Matakin Farko. Mamora ya ce a halin yanzu ba a yarda 'yan kasuwa su soma harkar shigo da allurar rigakafin korona ba. Ya ce gwamnati ba za…
09
Mar
Daga FATUHU MUSTAPHA Aƙalla baƙin haure 39 ne suka rasa rayukansu a lokacin da kwale-kwale biyu suka nitse a kusa da Tunisia a ranar Talata yayin da suke ƙoƙarin tsallake kogin Bahar Rum zuwa tsibirin Lampedusa na Italiya, in ji jami'an tsaron Tunisia. Jami'in Tunisa Mohamed Zekri, ya ce masu tsaron bakin ruwa sun samu nasarar ceto wasu mutum 165, sannan ana ci gaba da neman ƙarin waɗanda suka tsira a gaɓar Sfax. Ya ƙara da cewa dukkan baƙin hauren da suka mutun 'yan Afirka ne. Jaridar Alarabiya ta ruwaito cewa, a 2019 kimanin baƙin haure 'yan Afirka su 90…
09
Mar
Daga WAKILINMU Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin Zagon Ƙasa da Zambar Kuɗaɗe (EFCC) ta cafke wasu matasa 37 da aka fi sani da 'yahoo-yahoo boys' bisa zargin aikata damfara a intanet a Ado-Ekiti, jihar Ekiti. Hukumar da kanta ta bayyana hakan a wata sanarwar manema labarai da ta fitar ta hannun Shugaban Sashen Yaɗa Labaranta, Wilson Uwujaren, a Litinin da ta gabata. Sanarwar ta nuna EFCC ta yi nasarar kama matasan ne biyo bayan bayanan sirri da ta tattara kan harkokinsu na damfarar mutane ta intanet a yankin. Hukumar ta ce sakamakon binciken da jami'anta suka gudanar a…
09
Mar
Daga AISHA ASAS A Litinin da ta gabata Gwamna jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya karɓi allurar rigakafin cutar korona na AstraZeneca/Oxford guda dubu 50,000 a matsayin gudunmuwa daga Gwamnatin Tarayya. Maganin ya shiga hannun gwamnan ne a ofishinsa da ke Abeokuta, jim kaɗan bayan dawowar tawagar da ta wakilci jihar ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Lafiya na jihar, Dr Tomi Coker. Gwamnan ya shaida wa manema labarai cewa Ogun ita ce jiha ta farko da ta soma karɓar rigakafinta. Yana mai cewa allura ƙwaya 50,000 da ta samu rukunin farko ne na abin da take sa ran samu baki ɗaya. Ya ce…
09
Mar
Daga UMAR M. GOMBE 'Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 30 a Litinin da ta gabata a garin Kutunku da ke yankin ƙaramar hukumar Wushishi a jihar Neja. Wannan na zuwa ne bayan da Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya fito ya bayyana cewa daga yanzu babu wata tattaunawa da 'yan bindigar da ke yin garkuwa da mutane. Bayanai sun tabbatar cewa 'yan bindigar sun shiga ƙauyen Kutunku ne ɗauke da makamai kuma a qafa, inda suka yi wa ƙauyen zobe. Wata majiya ta ce, 'yan bindigar sun ɓoye baburansu a daji ne sannan suka ƙarasa ƙauyen a…
08
Mar
Shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa Kan Yaƙi da Cutar Korona (PTF), Boss Mustapha, tare da sauran mambobin kwamitin na PTF sun karɓi allurar rigakafin cutar korona. An yi musu allurar ne a lokacin da PTF ke gabatar da bayanan ayyukansa kanar yadda ya saba a Abuja. Mustapha wanda shi ne Sakataren Gwamnatin Tarayya, shi ya soma karɓar allurar wanda aka yaɗa kai tsaye a talabijin kafin daga bisani sauran jami'an suka karɓi tasu. Ministan Lafiya, Osagie Ehanire, shi ma na daga cikin waɗanda suka karɓi allurar.
08
Mar
Daga FATUHU MUSTAPHA Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari tare da sauran fitattun ‘yan Nijeriya sun taya Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo, murnar cika shekara 64 da haihuwa. Shugaba Buhari ya bayyana Osinbajo a matsayin mutum tsayayye wanda ba ya sake da ayyukansa. Buhari ya faɗi haka cikin wata sanarwa da ta fito ta hannun mai magana da yawunsa, Garba Shehu. A cewar Buhari, “Osinbajo mutanen mai sauƙin kai wanda ke kallon buƙatar Nijeriya a kan saura buqatu. Ɗan siyasa ne mai haƙuri kuma mai amfani da ilimi wajen aiwatar da ayyukansa.” Daga nan, Buhari yaw a mataimakin nasa fatan alheri tare…
