08
Mar
Daga BASHIR ISAH Matar Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari, ta yi kira ga masu faɗa a ji na Nijeriya da su ci gaba da yin amfani da damarmakin da suke da su wajen kawo ƙarshen harkokin yin garkuwa da mutane tare da tabbatar da cewa yara mata na da kariya a duk inda suka tsinci kansu. Aisha ta bayyana haka ne a saƙon taya murna ga 'yan'uwata mata kan Ranar Mata ta Duniya, da ta wallafa a shafinta na twita. Ta ce bikin ranar mata ta duniya, lokaci ne da kan bada damar a san irin nasarorin da aka…
