05
Mar
Daga UMAR M. GOMBE Etsu Nupe kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya na Jihar Neja, Alhaji Yahaya Abubakar, ya bayyana rasuwar marigayi Sarkin Kagara, Alhaji Salihu Tanko a matsayin babban rashi ga iyalan mamacin da masarautar Kagara da jihar Neja da ma ƙasa baki ɗaya. Etsu Nupe ya faɗi haka ne ga manema labarai a garin Minna a Larabar da ta gabata a lokacin da yake jajantawa game da rasuwar basaraken. Tare da cewa rasuwar marigayin ta haifar da wagegen giɓin da iya cike shi sai an yi da gaske. Da wannan ne sarkin ya ce, "A madadin Majalisar Sarakunan Gargajiya,…
