03
Mar
Daga FATUHU MUSTAPHA Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Ƙasa ta bayyana cewa a halin yanzu kimanin mutum milyan 2.6 ne suka rasa matsugunansu a faɗin ƙasa. Kwamishinan hukumar, Bashir Mohammed ne ya sanar da hakan a Litinin da ta gabata yayin ƙaddamar da shirin raba tallafin abinci ga mutum 7,500 waɗanda ibtila'i ya shafa a fadar gwamnatin jihar Kano. Garba ya ce 'yan gudun hijirar da ake da su a Kano mutane ne waɗanda matsalar tsaro da ambaliyar ruwa suka shafa daga jihohin Kudancin ƙasa. Ya ci gaba da cewa, Gwamnatin Tarayya ta kammala shirinta na sake tsugunar…
