13
Mar
Daga WAKILINMU Mambobin Ƙungiyar Matasa Magoya Bayan Tinubu (NYMT), sun yi kira ga jigon jam’iyyar APC, Asiwaju Ahmed Tinubu, da ya fito takarar neman shugabancin ƙasa a 2023. Matasan sun yi ra’ayin cewa babu wanda ya fi cancanta ya gaji Shugaba Muhammadu Buhari kamar Tinubu domin ci gaba ƙarfafa nasararorin da gwamnatin APC ta samu. A cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar a Abuja, Darakta Janar na ƙungiyar, Mukhtar Husseini ya jigon ya yi sadaukarwa sosai wajen ɗorewar dimukraɗiyyar da ake cin moriyarta a yau. Ya ce buƙatar mara wa Tinubu baya ta taso ne bisa la’akari da…
