Editor

9513 Posts
WTO: Ba domin Buhari ba da ban kaiblabari ba – Dr Ngozi

WTO: Ba domin Buhari ba da ban kaiblabari ba – Dr Ngozi

Daga FATUHU MUSTAPHA Shugabar Hukumar Cinikayya ta Duniya, Dr. Ngozi Okonjo-Iwela, ta ce taimako da goyon bayan da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi mata sun yi matuƙar tasiri wajen ba ta nasarar ɗarewa kujerar jagorancin hukumar WTO. Ngozi ta bayyana haka ne a lokacin da ta kai wa Buhari ziyara don nuna godiyarta, tana mai cewa zaɓin da Buhari ya yi mata wajen tsayawa takara da ɗaruruwan wasiƙun da ya rubuta wa shugabannin duniya da kiran da ya yi musu ta waya domin goya mata baya sun taimaka mata wajen samun nasara. Ta ci gaba da cewa da ba…
Read More
Dr Ngozi ta yi rashi

Dr Ngozi ta yi rashi

Mahaifin Dr. Ngozi Okonjo-Iweala, Farfesa Chukuka Okonjo, ya rasu. Marigayin ya bar duniya yana da shekara 91. Dr. Ngozi ita ce wadda a kwannan nan aka naɗa a matsayin sabuwar Shugabar Hukumar Cinikayya ta Duniya (WTO).
Read More
Rashin aiki a Nijeriya ya kai kashi 33.3, cewar NBS

Rashin aiki a Nijeriya ya kai kashi 33.3, cewar NBS

Daga UMAR M. GOMBE Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya (NBS), ta ce aƙaluman rashin aiki a Nijeriya sun sake cillawa, kamar yadda wani rahotanta ya nuna bada jimawa ba. Rahoton hukumar ya nuna an samu ƙarin adadi na rashin aiki a Nijeriya da ya kai kashi 33.3 cikin ɗari a zango na huɗu a 2020 saɓanin kashi 27.1 cikin ɗari a zango na biyu a 2020. NBS ta sanar da haka ne a cikin rahotonta da ta shirya kan sha'anin ƙwadago, tare da la'akari da matsalar rashin aiki musamman kuma a zamanin da ake fama da cutar korona, inda ta gano…
Read More
Idan da goyon baya mata kaɗai na iya ciyar da ƙasa – SWOFON

Idan da goyon baya mata kaɗai na iya ciyar da ƙasa – SWOFON

Daga BASHIR ISAH Kodinetar Ƙungiyar Ƙananan Manoma Mata (SWOFON) ta jihar Bauchi, Hajiya Marka Abbas, ta ƙarfafa cewa mata kaɗai na iya ciyar da ƙasa muddin suka samu goyon bayan da suke buƙata. Marka ta bayyana haka ne a wajen wani taron musayar ra'ayi game da harkokin noma, shiryawar ƙungiyar ‘Fahimta Women and Youth Development Initiative’ (FAWOYDI) tare da haɗin gwiwar ActionAid Nigeria, wanda ya gudana ran Litinin, a Bauchi. A cewarta mata sun fi maza iya tattali ta yadda za su iya amfani da kayan aiki kaɗan wajen samar da amfani mai yawa. Don haka ta yi kira ga gwamnati…
Read More
Jam’iyyar AAC ta fatattaki Sowore a ofishin INEC

Jam’iyyar AAC ta fatattaki Sowore a ofishin INEC

Daga FATUHU MUSTAPHA 'Ya'yan jam'iyyar African Alliance Congress (AAC) sun ce suna kan bakansu na korar da suka ce an yi wa Omoyele Sowore daga jam'iyyarsu har ma da neman 'yan sanda su kama shi saboda shigan burtun da suka ce ya yi musu. A wannan Litinin ne wani gungun mutane ƙarkashin jagorancin Sowore suka yi yinƙuri mamaye hedikwatar Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) a Abuja amma sai 'yan jam'yyar AAC ƙarƙashin jagorancin shugabansu na ƙasa, Dr. Leonard Nzenwa, suka fatattake su. Binciken Manhaja ya gano cewa, Sowore da mutanensa sun ziyarci ofishin INEC ne da nufin…
Read More
Tambuwal zai gina sakandare na zamani guda 40 a Sakkwato

Tambuwal zai gina sakandare na zamani guda 40 a Sakkwato

Daga AISHA ASAS Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Tambuwal, ya bayyana aniyarsa ta gina Makarantun Sakandare irin na zamani guda arba'in a sassan jiharsa. A wata sanarwa da ya fitar, Tambuwal ya nuna ilimi shi ne ƙashin bayan cigaba a cikin kowace al'umma. Ya ce ayyukan da gwamnatinsa ta sa gaba wajen inganta fannin ilimin jihar, da suka haɗa da yi wa makarantun firamare 1,500 da ƙananan sakandare 180 kwaskwarima, wata alama ce da ke nuni da yadda gwamnatinsa ta ɗauki fannin ilimin jihar da muhimmancin gaske. Kazalika, ya ce gwamnatinsa ta damu da batun yaran da ba su tafiya makaranta…
Read More
Don bai wa matsa aiki gwamnati ta ƙirƙiro aikin gina layin dogo a sassan ƙasa – Amaech

Don bai wa matsa aiki gwamnati ta ƙirƙiro aikin gina layin dogo a sassan ƙasa – Amaech

Daga UMAR M.GOMBE Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya ce babbar manufar Shugaba Muhammadu Buhari na gina layin dogo a sassan ƙasa ita ce don samar da aikin yi ga matasan Nijeriya. A Lahadin da ta gabata Minista Amaechi ya bayyana haka ta hannun hadimarsa kan sha'anin yaɗa labarai, Mrs Taiye Elebiyo-Edeni, yana mai cewa ayyukan samar da hanyoyin jirgin ƙasa da ke kan gudana za su taimaka wajen ƙarfafa tattalin arzikin ƙasa. Ya ce, bayan kammala layin dogo da ake ginawa a gabashin ƙasa hakan zai zama silar samar da gurbin aiki tsakanin 20,000 zuwa 50,000 baya ga sauran harkokin…
Read More
Mata 2,900 kowace za ta samu tallafin N20,000 a Binuwai

Mata 2,900 kowace za ta samu tallafin N20,000 a Binuwai

Daga AISHA ASAS Ministar Jinƙai, Agaji da Kyautata Rayuwar 'Yan Kasa, Sadiya Umar Farouq, ta jaddada aniyar Gwamnatin Tarayya ta neman fitar da talakawa da marasa galihun ƙasar nan daga ƙangin talauci. Ministar ta ce kimanin mata 2,900 ne gwamnati ta tallafa wa da kuɗi N20,000 ga kowannensu a jihar Binuwai ƙarkashin shirin musamman na Gwamnatin Tarayya na tallafa wa matan karkara a Binuwai da kuɗi don kama sana'a. Sadiya ta yi waɗannan bayanai ne a wajen bikin ƙaddamar da rabon tallafin ga matan karkara a Binuwai, in ji sanarwa da ta fito ta hannun Mataimakin Daraktan Labarai na ma'aikatar…
Read More
Ogun: Matar da ta babbaka mijinta da tafasasshen ruwa ta faɗa a komar ‘yansanda

Ogun: Matar da ta babbaka mijinta da tafasasshen ruwa ta faɗa a komar ‘yansanda

Daga WAKILINMU 'Yansandan Jihar Ogun sun cafke wata mata 'yar shekara 43 mai suna Bisola Awodele bayan da ta babbaka mijinta da tafasasshen ruwa, lamarin da ya yi wa mijin nata mummunan rauni a baya. Sanarwar manema labarai da Jami'in Hulɗa da Jama'a na 'yansandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi ya fitar a Abeokuta a ranar Lahadi, ta nuna Bisola ta faɗa a komar hukumar ce ranar 8 ga Maris biyo bayan rahoton da magidanta mai suna Peter Philip, ya kai a ofishin 'yansandan na yankin Sango Ota. Peter ya shaida wa 'yansandan cewa matarsa na zarginsa da yawan shan giya…
Read More
Adabi rayayyar kalma ce wadda ba ta mutuwa – Hauwa Lawal Maiturare

Adabi rayayyar kalma ce wadda ba ta mutuwa – Hauwa Lawal Maiturare

Hauwa Lawal Maiturare ba ta da buƙatar doguwar gabatarwa a duniyar rubutu. Sananniya ce ga waɗanda su ka fara karance-karancen littattafan Hausa wuraren 1998. Ta kasance cikin jerin marubuta da su ka shigo duniyar rubutu da ƙafar dama. Masu karatu za su tuna Maiturare da littafin ta na ‘Haske Maganin Duhu’ ko ‘Gobarar Gemu’. Wannan jarida mai farin jini ta yi nasarar kawo maku ita a wannan mako. Ku biyo mu don jin yadda tataunawar ta kasance. Daga AISHA ASAS a Abuja Mu fara da jin cikakken tarihin ki.Suna na Hauwa Lawal Maiturare wacce aka fi sani da Ƙamshi. Ni…
Read More