18
Mar
Daga FATUHU MUSTAPHA Hukumar yaƙi da rashawa ta ICPC ta cafke tsohon shugaban hukumar jarrabawar shiga jami'a (JAMB), Dibu Ojerinde bisa zargin badakalar Naira miliyan 900. Jami'an hukumar ne suka cafke Ojerinde ran15 Maris a Abuja bisa zargin aikata zambar kuɗaɗe a lokacin da ya shugabanci hukumar JAMB da kuma Hukumar Shirya Jarabawa ta Ƙasa (NECO). A cewar sanarwar da mai magana da yawun ICPC, Mrs. Azuka C. Oguguata fitar, ana tsare da wanda ake zargin. ICPC ta cafke Ojerinde bisa laifukan zambar kuɗaɗe ciki har odar sayo fensura da abun goge rubutu kan Naira miliyan 450 kowanne tsakanin 2013…
