19
Mar
Daga IBRAHIM SHEME Sau da yawa, na kan yi mamakin yadda wasu ’yan Nijeriya ba su so a zauna lafiya; kullum ƙoƙari su ke yi su tsokano wata magana da za a dinga tada jijiyar wuya a kan ta. Dubi dai tataɓurzar da ake yi kan batun saka hijabi na ’yan makaranta mata Musulmi a Jihar Kwara. Wasu Kiristoci sun tashi haiqan a kan cewa ba su yarda mata ɗalibai su sanya hijabi su je makaranta ba. Abin da ya fi ba ni mamaki shi ne masu wannan kamfen ɗin ba wai wasu zauna-gari-banza kaxai ba ne, waɗanda za a…
