Editor

9513 Posts
Dole ‘yan siyasa su soma yin rigakafin korona kafin talakawa su bi sawunsu, inji Sultan

Dole ‘yan siyasa su soma yin rigakafin korona kafin talakawa su bi sawunsu, inji Sultan

Daga UMAR M. GOMBE Mai Girma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya yi kira ga 'yan siyasa da su fito baina jama'a su yi allurar rigakafin cutar korona na AstraZeneca domin hakan ya zama ƙarfafawa da ƙwarin gwiwa ga sauran jama'a. Sarkin ya yi wannan kira ne yayin wani taron wayar da kai da aka shirya game da rigakafin cutar korona ga Musulmi a Juma'ar da ta gabata don faɗakar da malamai da kuma limamai. Basaraken ya yi kira ga al'ummar Musulmi da su je su yi allurar saboda a cewarsa, ta dalilin rigakafi ne Nijeriyar ta samu nasarar kuɓuta…
Read More
Akume ya ƙalubalanci masu gidajen caca kan tara wa gwamnati kuɗaɗen shiga

Akume ya ƙalubalanci masu gidajen caca kan tara wa gwamnati kuɗaɗen shiga

Daga WAKILINMU Ministan Ayyuka na Musamman, Sanata George Akume, ya buƙaci Hukumar Kula da Harkokin Caca ta Ƙasa (NRLC) da ta ƙara himma wajen tara wa gwamnati kuɗaɗen shiga domin ƙarfafa mata wajen yi wa ƙasa ayyukan cigaba da inganta tattalin arziki. Akume ya buƙaci hakan daga hukumar ne a Alhamis da ta gabata yayin wata ganawa da masu ruwa da tsaki a masana'antar caca a Abuja. Inda ya ce an rigaya an bai wa hukumar dama don yin abin da ya kamata. Ya ce, "Abin takaici ne ganin yadda ake tafka hasarar ta wannan ɓangare saboda babu abin da…
Read More
An taskace ‘yan Nijeriya miliyan 30 a Rajistar Al’umma ta Ƙasa, inji Minista

An taskace ‘yan Nijeriya miliyan 30 a Rajistar Al’umma ta Ƙasa, inji Minista

Daga WAKILINMU Gwamnatin Tarayya ta ce ta rubuta sunayen mutane da ba za su gaza miliyan 30 ba a Rajistar Al'umma ta Ƙasa (National Social Rajista, NSR) wadda za a yi amfani da ita a samu sauƙin ceto mutane miliyan 100 daga fatara a cikin shekaru 10 masu zuwa. Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ita ce ta bayyana haka a taron Sakatarorin Dindindin na jihohi kan shirin gwamnati na magance matsalolin yau da kullum (National Social Safety Nets Project, NASSP), wanda aka gudanar a ranar Alhamis a Abuja. Ministar ta samu wakilcin Sakataren Dindindin…
Read More
‘Yan wasa 8000 ne za su fafata a bikin wansannin motsa jiki na Edo – Minista

‘Yan wasa 8000 ne za su fafata a bikin wansannin motsa jiki na Edo – Minista

Daga UMAR M. GOMBE Gwamnatin Tarayya ta bada tabbaccin za a gudanar da bikin wasannin motsa jiki da aka shirya gudanarwa a jihar Edo kamar yadda aka tsara. Ministan Harkokin Matasa da Wasannin Motsa Jiki, Chief Sunday Dare ne ya bada wannan tabbaci a garin Benin, Juma'ar da ta gabata. A cewar Dare, bikin wanda ake sa ran ya ƙunshi 'yan wasa 8000, zai gudana ne daga ranar 2 zuwa 4 ga Afrilun 2021. Da yake jawabi bayan kammala zagayen duba kayayyakin wasa da kuma ganawa da gwamnan jihar, Godwin Obaseki, Ministan ya ce, "za a buɗe sansanin 'yan wasa…
Read More
AMAC: Candido ya ɗauki nauyin karatun yara 29

AMAC: Candido ya ɗauki nauyin karatun yara 29

Daga AISHA ASAS Shugaban Hukumar Abuja Municipal (AMAC) Abdullahi Adamu Candido, ya yi alƙawarin bada tallafin karatu na musamman ga ɗaliban firamare su 29 da suka shiga gasar baje fasahar rubutun insha'i na bikin Ranar Farin Ciki ta Duniya na 2021 da kuma ƙaddamar da littafi wanda ya gudana a sakatariyar Hukumar Makarantun Firamare (LEA) da ke Wuse, Abuja. Shugaban ya sanar da haka ne a wajen wani taron bita ga manema labarai wanda ya gudana a Keffi, Jihar Nasarawa. Candido ya ce tuni an ware kuɗi naira milyan N26 domin cika wannan alƙawari da ya ɗauka na bada tallafin…
Read More
Na zama marubuci tun a ranar da na fara iya karatu da rubutu – Abul-Waraƙat

Na zama marubuci tun a ranar da na fara iya karatu da rubutu – Abul-Waraƙat

A yau wannan fili ya yi babban kamu inda ya karɓi baƙuncin fasihi kuma haziƙin marubuci kuma mawaƙi, wato Binyaminu Zakariya, wanda saboda hazaƙar sa da basirar sa ake yi masa laƙabi da Abulwaraƙat, wato baban takarda. Binyamin Zakariyya ya bayyana cewa ya fara rubutu ne tun daga lokacin da ya fara iya rubutu, wato ya na ƙaramin yaro. Haziƙin ya ƙware wajen rubuta waƙa da rubutun hikaya a harshen Larabci da Hausa. Ku biyo mu don jin yadda tattaunawar mu da shi ta kasance. Daga IBRAHIM HAMISU Kano Masu karatun mu za su so sanin taƙaitaccen tarihin ka.Suna na…
Read More
Halifan Tijjaniyya: Sunusi ya gaji Sunusi

Halifan Tijjaniyya: Sunusi ya gaji Sunusi

Daga FATUHU MUSTAPHA A makon da ya gabata ne aka yi taron shekara-shekara na mauludin tunawa da Shehu Ahmad Tijjani a Birnin Sakkwato. Taron da ya samu halartar dubban mutane da sassa daban daban na duniya, ciki kuwa har da wasu gwamnonin qasar nan, da suka haxa da Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal, na Zamfara Bello Matawalle, tsohon Gwamnan Jihar Imo, Mista Rochas Okorocha da sauran su. Haka kuma mai martaba Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ma ya samu damar halartar taron, da kuma manyan malaman ɗariƙar daga ciki da wajen wannan ƙasa. A yayin wannan taro dai, an kuma…
Read More
Muzguna wa Mahdi Shehu barazana ne ga yaƙin da Buhari ke yi na daƙile cin hanci

Muzguna wa Mahdi Shehu barazana ne ga yaƙin da Buhari ke yi na daƙile cin hanci

Daga ALIYU ADAMU TSIGA Cutar da Gwamnatin Jihar Katsina ke yi wa wani mai fallasa bayanan sirri, Mahdi Shehu, na yin barazanar yaƙi da cin hanci da rashawa na Shugaba Muhammadu Buhari, a cewar wata ƙungiyar farar hula. Ƙungiyar 'Movement for Good Governance and Greater Nigeria' (MGGGN), gamayyar ƙungiyoyin fararen hula da ke ƙoƙarin ganin bayan cin hanci da rashawa da samar da shugabanci na gari a ƙasar, a cikin sanarwar bayan taron da ta fitar a majalisar zartarwa na kasa da ta gudanar a Abuja a karshen mako, ta yi tambaya kan yakin da gwamnati ke yi da cin…
Read More

Yadda ’yan bindiga suka kashe Sojoji 4 da ƙona motar su a Zamfara

Matawalle Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne da ba su tuba ba sun afkawa ƙauyen Kabasa da ke Gundumar Magami a Ƙaramar Hukumar Gusau ta Jihar Zamfara, sun kashe mazauna ƙauyuka biyar da kuma sojoji uku da suka haɗa da Manjo wanda Kwamanda ne dake wakiltar Yankunan Magami, Dankurmi da Dansadau tare da ƙone motar sojojin. Wani mazaunin yankin mai suna Malam Lawali Magami a wata hira ta wayar tarho tare da Manhaja a Gusau ya ce, ’yan ta'addan sun yi wa ƙauyen qawanya da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin ranar Talata, suka fara…
Read More

‘Yan bindiga sun yi niyyar halaka ni ne – Sarkin Birnin Gwari

Alh. Zubairu Jibril Daga MUHAMMAD AHMAD a Kaduna A sakamakon harin da wasu ’yan bindiga suka kai wa tawagar  Sarkin Birnin Gwari, Alhaji Zubairu Jibril Mai Gwari II, sarkin ya ce an yi niyyar halaka shi ne, amma sai aka samu kuskure ba ya cikin motar tasa. Sarkin ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan harin da aka kai wa tawagar tasa a jiya Alhamis, a kan hanyar su ta zuwa Kaduna domin yin taro da gwamnan jihar, yana mai cewa akwai haɗin bakin wasu daga cikin al’ummar Birnin Gwari. Alhaji Zubairu Jibril Mai Gwari II ya ce “Akwai kyakkyawan…
Read More