23
Mar
Daga UMAR M. GOMBE Gwamnatin Tarayya ta bada haske kan wasu matakan da ta ɗauka domin tabbatar da Nijeriya ba ta yi fama da ɓarkewar annobar korona karo na uku ba. Yayin da wasu ƙasashen duniya suka soma sake fama da bugun annobar karo karo na uku, Ministan Lafiya, Dr Osagie Ehanire ya ce Nijeriya za ta ci gaba da aikin gwaje-gwaje da take yi domin ganowa, killacewa da kuma kula da waɗanda suka kamu da cutar. Ehanire ya bayyana haka ne a Litinin da ta gabata a Abuja yayin da kwamitin Shugaban Ƙasa kan Yaƙi da Cutar Korona ke…
