25
Mar
Daga FATUHU MUSTAPHA Gwamnatin Tarayya ta gabatar da ƙudirin ƙirƙiro da masana'antar cikin gida guda ɗaya a kowace ƙaramar hukuma daga ƙananan hukumomi 774 da ake da su a ƙasar nan. Gwamnatin ta ce tana sa ran kashe kuɗi naira tiriliyan N1 ne domin cim ma wannan ƙudiri. Ministan Ayyuka na Musamman, Sanata George Akume ne ya bayyana hakan yayin ganawarsu da Kwamitin Majalisar Dattawa Kan Ayyuka na Musamman. Inda ya ce irin wannan masana'anta ta cikin gida za ta maida hankali ne wajen samar da kayayyakin masarufi don amfanin al'ummar yankin da aka kafa masana'antar a cikinta. Da yake…
