26
Mar
Daga IBRAHIM SHEME A ranar Talata, shugaban riƙo na jam’iyyar APC na ƙasa, Mai Mala Buni, ya faɗi wata magana wadda ta bar baya da ƙura. A cewar sa, jam’iyyar za ta ci gaba da mulkin Nijeriya har zuwa shekaru 32 masu zuwa; wato dai, har zuwa shekara ta 2053. Idan ka haɗa da shekaru shida da ta yi daga 2015 zuwa yau, za ka samu shekara 38 kenan. Na so a ce Mai Mala Buni ya faɗa mana kuma yadda mulkin jam’iyyar zai ƙare a cikin 2053 tunda dai a nan ya yi mata iyaka. Shin a lokacin ne…
