Adabi rayayyar kalma ce wadda ba ta mutuwa – Hauwa Lawal Maiturare

Hauwa Lawal Maiturare ba ta da buƙatar doguwar gabatarwa a duniyar rubutu. Sananniya ce ga waɗanda su ka fara karance-karancen littattafan Hausa wuraren 1998. Ta kasance cikin jerin marubuta da su ka shigo duniyar rubutu da ƙafar dama. Masu karatu za su tuna Maiturare da littafin ta na ‘Haske Maganin Duhu’ ko ‘Gobarar Gemu’. Wannan jarida mai farin jini ta yi nasarar kawo maku ita a wannan mako. Ku biyo mu don jin yadda tataunawar ta kasance.

Daga AISHA ASAS a Abuja

Mu fara da jin cikakken tarihin ki.
Suna na Hauwa Lawal Maiturare wacce aka fi sani da Ƙamshi. Ni ‘yar asalin Jihar Kano ce. An haife ni a Ƙaramar Hukumar Dala da ke cikin Birni. Na fara da karatun Muhammadiyya bisa ga al’ada, sannan na ɗora da karatun zamani na firamare. Na yi sakandaren ‘yan mata ta garin Ƙwah, daga baya na dawo makarantar sakandare ta ‘yan mata ta Dala (GGC Dala), Kano. Na ci gaba da Kwalejin Horas da Malamai ta Tarayya da ke Kano (FCE) don samun shaidar malanta mai daraja ta ɗaya. Daga baya na ɗora daga inda na tsaya zuwa karatun digiri na farko (B.Ed Hausa) a Jami’ar Bayero. Yanzu haka ina ci gaba da karatun digiri na biyu a kan Adabin Hausa. Na tava aure. Ni malamar makaranta ce, kuma marubuciya.

Rubutu ya shiga wani kwazazzabon da wasu ke ganin ba ta yadda za a iya fito da shi, har ya dawo da ƙima da darajar sa. A matsayin ki na ƙwararriya kuma wadda ta jima a duniyar rubutu, yaya ki ke hangen wannan hasashen?
Kalmar adabi rayayyar kalma ce wacce ba za ta tava mutuwa ba sai ranar da al’umma ta ƙare. Kin ga kuwa ba wanda zai ce ga ranar da al’ummar Hausawa za ta ƙare, sai dai shi ya faru ya gama zamanin sa ya ƙare. Haka abin ya ke ga rubutu. Tunda kuwa rubuce-rubucen ƙagaggun labarai ana yin su ne da harshen Hausa, kuma su na waƙiltar Hausawa ne, to kuwa rubutu ba zai taɓa zama shafaffe ba, sai dai a samu sauyin yanayi ta wata fuskar. A yanzu akwai muhimman al’amura da su ka shafi rayuwar al’umma da ɗaukar hankali wanda marubuta za su iya ɗaukar alƙalami su yi rubutu a kai, haka nan bayan makaranta litattafai akwai ɗalibai na nazari da su ke nazartar aikace-aikacen su. Wannan dalili ya sa na ce rubutun ƙagaggun labaran Hausawa ba zai taɓa rasa daraja ba a yau har ma a gobe.

Wasu na ganin rashin haɗin kai na marubuta ne ummulhaba’isin matsalolin da su ke fuskanta a yanzu. Ya zancen ya ke a mahangar ki?
Matsalolin da ke faruwa wajen ɗan daƙile harkar rubutu shi ma ya na da nasaba da mawuyacin halin da tattalin arzikin ƙasa ya faɗa ne. Kawai abin da zan ce a ƙarshe marubuta su kyautata rubutun su, sannan su zakƙulo matsalolin da ke damun al’umma da ƙasa baki ɗaya su yi rubuce-rubucen su a kai, kama daga matsalar fyaɗe, rashin tsaro, matsin tattalin arziki, dogaro da kai ta fuskar sana’a ba ta fuskar gwamnati ba, kyautata zamantakewa, ilimi, lafiya, da dai sauran su.
Marubuta kuwa na da haɗin kai da girmama juna; da wahala a ce yau ga wasu marubuta sun fito su na ka-ce-na-ce da junan su. Kowannen mu na girmama juna, sannan ana ƙokƙarin biyayya ga ƙungiyoyi da dokokin su. To kin ga a nan marubuta tsintsiya ne maɗaurin mu guda, kamar abin da na ce matsi na tattalin arziki ya taimaka wa rauni a bunƙasar su, sannan rashin samun tallafi daga gwamnati ma ya taimaka kamar yadda marubuta zubin farko su ka samu, amma duk da haka haɗin kan marubuta na ƙara taimaka musu wajen ƙara jin amon su da na alqaluman su, ba wai taimakawa ya yi wajen daƙushe su ba.

Kin yi zancen tallafi daga gwamnati. Ta yaya gwamnati za ta taimaki marubuta?
Kasancewar gwamnati inuwa rumfar kowa marubuta kamar takwarorin su masu ayyukan fasaha ta yadda za ta samar da wani tallafi na kuɗi da kayan aikin ɗab’i ga marubuta kawai, tare da shirya tarurruka na wayar da kai gare su da bijiro da muhimman batutuwa da su ka shafi raya ƙasa, marubuta su yi rubutu a kai, a taskace waƙannan rubuce-rubucen a yi musu bugu mai inganci a rarraba su ga makarantu da ɗaliban ilimi domin nazari, sannan a ba wa waɗannan marubuta ɗan wani abu da zai ƙara musu karsashi ba wai don biyan su ba. Wannan zai taimaka ta fuskoki da dama. Sannan a samar da hanyar daftare rubuce-rubucen su da watsa shi ga hannun jama’a, zai taimaka wa marubuta damar fitowa da yin gogayya a fagen rubutun, sannan zai taimaka wajen yin rubuce-rubuce masu inganci da kalailacewa kafin ɗab’i kamar yadda marubutan dauri irin su Abubakar Imam su ka samu irin wannan tallafin.

Ya za a inganta martabar adabi?
Yadda  za a ƙara kyautata martabar adabi, marubuta su riƙa nitso wajen zaƙulo muhimman al’amura da su ka shafi rayuwa ta kowane fanni, sannan su kyautata rubutu ta hanyar bin ƙa’idojin rubutu da shirya manufofin su daki-daki yadda ya kamata, sannan da guje wa dukkan abin da zai ci karo da munana addini da al’ada.

Littattafai sun yi ƙaranci a kasuwa saɓanin ‘yan shekarun baya. Ko menene dalili?
Ya na daga dalilin matsin tattalin arziki a ƙasa. Hajiya, ana ta shinkafa da tattasan miya wa ya ke ta takarda?

Waɗanda su ke son fara rubutu har su mayar da shi littafi ta ina za su fara?
Shawarar da zan ba wa matasan marubuta ita ce, “da na gaba ake gane zurfinruwa”. Su yi qoqarin koyi da salon magabata wanda zai ƙara musu kaifin basira tare da buɗe musu hanyoyi na ɗorawa daga inda na baya su ka tsaya. Su yi rubutu da kyau a kan jigogi muhimmai waxanda za su ƙara wa rayuwa cigaba. Su guje wa yi wa addini da al’ada karan-tsaye. Su kuma riƙa bincike kafin aiwatar da rubutu, domin a san da su ka ɗauki alƙalami su ka yi rubutu sannan ya ke nasu, amma da  zarar sun sake shi to ya zama ba nasu ba. Su tuntuɓi magabata da masu ruwa da tsaki a harkar rubutu da fitarwa za su samu a hanyar da ta kamata. Kin san Bahaushe ya ce matambayi ba ya ɓata.

A wane lokaci ki ka fi jin daɗin rubutu?
Na fi jin daɗin yin rubutu lokacin hantsi, babu yawan hayaniya, magidanta da yara kowa ya kama ayyukan gaban sa, babu gajiya da rashin hutu domin an riga an yi da daddare.

Menene burin ki a fagen rubutu nan gaba?
Buri na a fagen rubutu alqalami na ya isa duniyar da ni ban je ba, kuma ya kasance manufofin da na yi rubuce-rubuce a kan su su amfanar da jama’a.

Wace shawara za ki ba wa mai son fara rubutu?
Shawara ga mai fara rubutu ya zama mai manufa mai kyau, ya kasance mai bincike a yayin gudanar da rubutu a kan kowane jigo/saƙon da ya ke son rubutu a kai. Ya kuma tuntuvi marubuta ko masu alaƙa da rubutu don ƙarin samun haske.

Me za ki ce dangane da rubutun da ake cewa su na lalata tarbiyyar ‘ya’yan mu, wato rubutun batsa?
Ina Allah-wadai da shi kasancewa ta uwa, ‘yar’uwa, malama, mai nusar da al’umma kullum buri na mutane su kyautata ɗabi’u da halayya, su yi biyayya sau da ƙafa da dukkan wasu dokoki na addini. Lallai addini ya umarce mu da mu zama masu ɗa’a. Waɗanda su ke ire-iren waxannan rubuce-rubucen su ji tsoran Allah.

Wace shekara ki ka fara rubutu?
Na fara rubutu tun 1998.

Wanne ne littafin ki na farko?
 ‘Biyayya’.

Wani babban ƙorafi da ake yi a kan littattafan Hausa shi ne rashin ƙa’idojin rubutu. Shin me ya sa har yau ba a kawar da wannan matsalar ba?
Abin da mutane su ka kasa fahimta shi ne rubutu baiwa ce, ba wai ilimi ba. Akwai da yawa daga marubuta da karatun bai yi zurfin da za a iya bambance tsaba da tsakuwa ba, duk da yake dai ana ƙoƙari matuƙa, sannan ƙungiyoyin marubuta su na shirya tarurruka na ƙara wa juna sani, su na ƙoƙari matuƙa wajen wayar da kai da ilimantar da mambobin su kan dabarun gyara rubutu wanda ya haɗa da koyar da abin da ki ke faɗa. Alhamdu lillahi kuma ana sa ran kullum laya ta yi ta kyan rufi.

Hamdan lillah, mu na godiya.
Ni ma haka.