Asara ce mace ta riƙe wayar N50,000 ba ta kawo mata N5,000 – Ayat Adamu 

“Idan ka ji shiru a gidan aure, ba ƙorafi, matar na sana’a”

Daga AISHA ASAS 

(Ci gaba daga makon jiya)

Mai karatu barkanmu da sake ganin zagayowar sati lafiya. Idan ba ku shafa’a ba, a satin da ya gabata, mun ɗauko tattaunawa da fitacciyar ‘yar kasuwa mai kishin matan Arewa, Ayat Uba Adamu. Inda muka soma da jin tarihin rayuwarta, zuwa irin sana’ar da take yi, kafin mu tsunduma kan yadda take gudanar da kasuwancin nata.

A tattaunawar, Hajiyar ta sheda wa Manhaja irin yunƙurin da ta yi na kafa ƙungiya musamman domin mata masu kasuwanci da ke tu’ammali da kafafen sadarwa, kafin mu ja birki kan tambayar da muka yi wa masu karatu alƙawarin samar masu da amsarta daga gare ta kafin wasu tambayoyin su biyo baya. 

Idan kun shirya, har wa yau dai Aisha Asas ce tare da Hajiya Ayat Uba Adamu:

MANHAJA: Zuwa yanzu za a iya cewa kwalliya ta fara biyan kuɗin sabulu dangane da kamfanin naki?

HAJIYA AYAT: Eh ta fara biyan kuɗin sabulu, domin duk da har yanzu ban samu injimin sarrafa tomatoes paste ɗin ba, amma an samu na sarrafa shi ya zama bushashen garin tomatir, kuma muna nan muna ta gwaji, wanda muna sa ran alheri ne insha Allah.

Shi wannan tumaturi da ake sarrafa ya zama ‘ɗan kanti’ da sauran kayan gona da kamfanin naki ki yi, ko ana iya samun su a shaguna na siyar da kayan abinci, koko dai duk wanda ke bukata sai ya biyo ta ɓangaren ki?

A yanzu iya garin tamba ake iya samu shi ma a iya shagonmu da ke zoo road, sai ko masu siya a kafafen sadarwa, domin ba mu fara kai shi manyan kantuna ba, muna son ƙarasa cike dukkan sharuɗɗa da suka kamata. 

Mu koma kan zancen ƙungiyar da ki ka asassa. Mutane da dama, musamman masu tu’ammali da kafafen sada zumunta sun ci karo da wannan ƙungiya ta ‘Women Online Vendors Association’, sai dai ba kowa ne ya san ainahin manufofin kungiyar ba. Ko za ki yi mana qarin haske kan ita kanta ƙungiyar da kuma dalilin kafa ta?

An samar da ita ne domin samun mafita ga mu mata masu kasuwanci a yanar gizo , wanda akwai damarmaki amma ba za a samu ba sai a dunƙule guri ɗaya. Sannan kayan mu su zaga duniya, ta hanyar ‘website’ ɗin mu, yadda dukkan wata member za a ɗora kayanta, kuma duk inda mutum yake a duniya yana shiga zai gani, zai siya. Manufofin suna da yawa. Kaɗan daga ciki akwai;

1.Samar da hanya mafi sauƙi ta isar da kayanmu da ka siya ga mai shi (del)

  1. Wayar da kan mata kan muhimmancin inganta sana’a da zamanantar da ita.
  2. ƙarawa juna ilimi ta hanyar shirya ‘conference’, ‘seminar’, inda masana za su koyar da ilmantar da mu matan kan sana’ar mu da kuma abinda zamani yazo da shi kan sana’a. 
    4 . Nema wa mata tallafi da nemo wa mata damarmaki daga hukumomin da aka samu dama, ciki har da wasu daga ɗaiɗaiku mutanen ( wasu ma suna nan sahar facebook kuma suna taimaka mana sosai. Allah ya saka musu da alheri). 

Kin kasance ‘yar kasuwa, ma’aikaciyar lafiya kuma jigo a ƙungiyar WOVA. Shin ya ki ka iya haɗa taura biyu ki tauna su a lokaci guda?

Alhamdulillah, ba abinda za mu ce wa Allah sai godiya. Duk wannan abinda ki ka ambata cikin ikon Allah haka ake aiwatar da su. Kinga aikina na asibiti ba kullum ba ne, akwai iya ranakun, ita kuma WOVA muna da ma’akaciyar mu a office ɗin na ƙungiyar, duk wani abinda ya shafi office tana nan idan an je za a sameta. Wanda kuma ya zama lallai sai mun yi da kan mu, yanzu kinsan muna cikin wani lokaci da ‘technology’ ya yawaita don haka wani aikin ma da wayoyinmu za mu yi shi. Kin ga wannan ko ina mutum yake zai iya. Babban sirrin kuma shi ne ‘support’ da na samu daga maigida ne, duk wannan abin da ban samu goyon bayansa ba, ba lallai na yi nasara ba, shima Allah ya saka masa da alheri .

Wasu mata da ke zaune ba wani abin dogaro da kai da suke yi, sukan yi ƙorafin rashin jari ne ya hana su sana’a. A wani ɓangare kuwa an samu rarrabuwan kai, inda wasu ke ganin a wannan zamani da muke ciki rashin jari ba zai iya zama hujjar da za ta iya hana mutum sana’a ba. Yayin da wasu ke ganin har gobe jari ne jigon kowacce irin sana’a. Menene naki ra’ayi?

A nawa ra’ayin ya danganta da wanne burin ake dashi, wata jarin ₦5,000 ko ₦10,000 ya ishe ta kuma zata sarrafa ta juya abinta, wata kuma sai ₦100,000 wata sai ta ce, sai miliyan, Kinga abin ai ya danganta da ra’ayin mace da irin burin ta, amma idan mace na riqe wayar ₦50,000 kuma wannan wayar ba ta kawo mata ₦5,000 a wata ai ba karamar asara ba ce. Kinga ita ke kashewa wayar kuɗi kenan, amma idan ta samu sana’a tana yi, tana kuma tallatawa online ai za ta samu kasuwa daidai gwargwado.

Ko sana’a na taka muhimmiyar rawa a zamantakewar aure?

Ƙwarai kuwa, idan ki ka ji shiru a gidan aure ba korafi ba yaji, ai akwai abin yi, wato mace na sana’a ba ta da lokacin gulma, ko yawo gidan ƙawaye da maƙwabta don haka za a samu zaman lafiya ita da mijinta, hankalin ta na kan mijinta da yaranta da sana’ar ta. Randa ba shi da shi za ta ɗauko a nata ayi abinda ya dace, amma idan mace bata sana’a roƙo ma ya ishe mijin, wanda mafi yawan maza ba sa son yawan ba-ni-ba-ni, ballanta a wannan lokacin na matsin rayuwa da muke ciki. 

Don haka kowacce mace ta nemi sana’a, ko da kuwa kina aikin gwamnati ko na kamfani ya kamata a haɗa da sana’a domin kafin lokacin da za a bar aikin an ginu da sana’ar ko da zaman gida ya zo (wato ba fita aiki anyi ritaya) an ginu an gama rainon sana’ar sai zaman yai daɗi ba za a gundiri yara ko ‘yan’uwa da ba ni- ba ni ba.

A wannan gavar ne ma nake wa mata albishir, akwai ‘conference’ da WOVA ta shirya za tai a watan Disamba, insha Allah, wanda a wannan taron masana za su yi bayanin yadda mace za ta yi amfani da ‘technology’ wajen kasuwancin ta, wanda muke sa ran ma’aikatan gwamnati da kamfanoni mata za su halarta insha Allah, domin su yi amfani da ilimin wurin morar goben su, wato bayan ritaya.

Kin yi maganar taro na ƙarawa juna sani da ƙungiyar taki za ta shirya. Ta wacce hanya ce mata masu sana’a ko shirin fara sana’a za su iya samun damar kasancewa a taron?

Akwai link (rariyar liƙau) da muka samar wanda ta hanyar wannan link za a shiga ayi ‘registration’, sannan idan ke member ce ta WOVA za ki biya ₦5,000 kuɗin ‘registration’, wadda kuma ba mamba ba ₦6,500 za ta biya na rijistar. Sannan akwai ‘certificate’ da za a ba wa duk wacce ta halarci taron, wanda shi wannan taron zai zama mabudin ido ne ga gare mu bakiɗaya akan kasuwanci, wanda kuma taron zai zama kururuwa ga hukumoni waɗanda ya dace su ji mu su kawo mana ɗauki, duk da yanzu ma an fara kawo mana ɗaukin.

Wacce shawara za ki ba wa matasa kan amfani da kafafen sadarwa wurin neman na kai?

Ina ba su shawara da su gane cewa, ba sai anyi rashin daraja ake suna ba, su daure su yi amfani da ƙuruciyar su, da lokacin su, su inganta rayuwarsu ta hanyar neman ilimi ko kasuwanci a waɗannan kafafen na sada zumunta na zamani.

Mene ne burinki a wannan sana’a da ki ke yi.

Babban burina shi ne, na samar da ingantaccen garin kunun Tamba, da garin kayan miya mai inganci, sannan kuma na samar da aiki ga mata da matasa. 

Daga ƙarshe wacce shawara ki ke da ita ga mata ‘yan uwanki bakiɗaya?

Mu zauna lafiya da mazajenmu, iyalanmu, domin zaman lafiyar ki da iyalinki ya na daga sirrin nasarar sana’arki, domin sai da kwanciyar hankali ake komai, ake gane komai. Kuma kar mu raina sana’a ko mai kankantar sana’a tana da amfani ƙwarai ga gaske. Allah ya albarkaci rayuwarmu da ta iyalanmu. Allah ya albarkaci kasuwancimu.

Mun gode.

Na gode.