Zaɓuɓɓukan 11 ga Nuwamba: Za mu yi watsi da ƙuri’un duk rumfar zaɓen da aka samu hayaniya – INEC

Daga BASHIR ISAH

Yayin da rage ‘yan kwanaki ƙalilan kafin zaɓen gwamna a wasu jihohin Nijeriya, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta yi gargaɗin ba za ta kula ƙuri’un duk wata rumfar zaɓe da aka fuskanci tashin-tashina ba.

Shugaban INEC, Mahmood Yakubu ne ya yi wannan gargaɗi yayin taron masu ruwa da tsaki da ya gudanar ranar Talata a Yenagoa, babban jihar Bayelsa.

Ya zuwa ranar 11 ga Nuwamban da ake ciki ne ake sa ran INEC za ta gudanar da zaɓen gwamnoni a jihohin Bayelsa, Kogi da kuma Imo.

Yakubu, wanda ya samu wakilcin Kwamishinan INEC mai lura yankunan Akwa-Ibom, Bayelsa da Ribas, May Agbamuche-Mbu, ya bayyana cewa INEC za ta tuea na’urar BIVAS zuwa ɗaukacin rumfunan zaɓe yayin zaɓen.

“Ina so ku sani cewa, an sarrafa na’urar BIVAS don amfanin INEC kwaai, don haka an zuba bayanan INEC da sunayen jam’iyyun siyasa cikin na’urorin, saboda haka duk na’urar BIVAS da aka tarar babta ɗauke da bayanan INEC, ba daga INEC ta fito ba,” in ji Yakubu.

Ya ƙara da cewa, an ɗauki ingantattun matakai don tabbatar da zaɓukan sun gudana cikin nasara.