Bayan tsaftace ƙasa daga fasadi sai a waiwayi yunwa

Manhaja logo

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A lokacin da nake wannan rubutun, jami’an Hukumar Hisba ta Jihar Kano na can na aikin tantance matasan da jami’anta suka kama bisa laifin aikata fasadi, yawon dare, da mu’amala a wuraren da suke ɓata tarbiyyar al’umma, biyo bayan samame da suke kai wa a wasu gidajen karuwai, kulob-kulob, da ɓoyayyun wuraren da ɓatagari ke fakewa suna aikata ɓarna cikin dare a sassa daban-daban na cikin birnin Kano.

Sannan a wata tattaunawa da tashar rediyon Freedom ta yi da wasu daga cikin waɗannan matasa sun bayyana wuraren da aka kama su, da abubuwan da suka ce suna yi a lokacin samamen da aka kai. Yayin da wasu suka amsa cewa, lallai an kama su suna aikata ba daidai ba, kuma sun yi nadamar abin da suke yi. Wasu kuma sun bayyana cewa, azal ce ta afka musu a daidai lokacin da aka je yin kamen, amma ba don sun je aikata wani abin assha ba. Dama kuma hakan na iya faruwa, a kai samamen kan mai uwa-da-wabi a kama masu laifi da marasa laifi, sai daga baya ne za a ware kowa ya amsa sunansa. Hakan kuma yana zama darasi ga waɗanda hakan ta faru da su, da kuma waɗanda suka kuvuta, ba su da rabon shiga komar ’yan Hisbah.

Tun da farko mun ga wani bidiyo da ake yaɗawa a kafofin sadarwa na zamani, da ke nuna yadda wasu da ake ganin jami’an Hisbah ne suke cakumar wasu da aka kama suna wurgawa bayan wata Hilux da aka yi amfani da ita wajen tattara waɗanda aka kama, ciki har da wasu ’yammata da aka yi wa ɗiban karan mahaukaciya aka watsa su cikin motar. Abin da ya jawo cece-kuce a tsakanin jama’a, da ke nuna hakan bai dace ba. Ganin cewa mata ne, kuma su jami’an wakilai ne na wata hukuma ta addini, sannan a wannan lokacin suna matakin zargi ne ba masu laifi ba ne. Don haka ya kamata a mutunta waɗanda ake kamawa ana zargi, a matsayinsu na ’yan Adam, masu ’yanci da daraja, kamar yadda yake bisa tsarin doka.

Kodayake ba wannan ne lokaci na farko da jami’an Hukumar Hisbah ke kai irin wannan samame ba, musamman a unguwar Sabon Gari, inda wuri ne da ake yi wa ganin matattara ce ta vatagari da masu mummunan aiki. A wani vangare na sauke nauyin da dokar Jihar Kano ta ɗora musu na yaqi da ayyukan baɗala da fasadi a faɗin jihar, wacce ke amfani da shari’ar Musulunci. Sai dai a wannan karon ayyukan nasu sun faɗaɗa, zuwa wasu cibiyoyi na nishaɗi da taruwar matasa, wanda dama an daɗe ana sa ido a kansu.

Na samu shiga cikin wani aiki makamancin wannan da hukumar tsaro ta Civil Defense ta Jihar Gombe ta jagoranta da haɗin gwiwar Majalisar Malamai ta jihar, domin yaƙi da bazuwar gidajen karuwai, gidajen Gala, da cibiyoyin baɗala da ake buɗewa, wanda ke zama matattarar ɓatagari, ɓarayi da ’yan fashi da suka addabi jihar. Na ga yadda aka yi kamen da tsare ’yammatan da ake zargi da barin gidajen iyayensu ko garuruwansu na asali, suna tarewa a wasu wurare marasa tsafta, da basu dace da kimarsu da mutuncinsu ba. Wasu ma an same su da kayan maye, wasu daga cikin ’yammatan ma suna da goyon ’ya’yan da ba a san asalinsu ba, wasu na da ciki, wasu kuma bayan bincike an gano suna ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki. Har ma da wata da aka kama ana saura kwanaki a ɗaura mata aure, amma ta fita shaƙatawa da wasu mazan banza.

Ba ina son mayar da hankali kan wannan samame na ’yan Hisbah a Kano da Gombe ba ne kawai, ina so ne in ja hankalinmu kan muhimmancin waɗannan ayyuka da hukumomi ke yi na tabbatar da ganin sun tsaftace al’umma daga ɓarna da kuma yaƙi da masu aikata laifuka ko baqi da ke aikata laifi a wasu jihohin suna zuwa suna ɓoye kansu a irin waɗannan wurare. Barin irin waɗannan ɓatagari lallai babban kuskure ne, da ke ƙara ta’azzara lalacewar tarbiyya, ƙaruwar aikata laifi, yaɗuwar cututtuka, da lalacewar doka da oda.

Sai dai a lokacin da hukumomi ke aiwatar da irin wannan aiki na gyaran tarbiyya, ya kamata su sani cewa, ita fa tarbiyya tun daga gida take lalacewa. Lallai ne idan an tashi ƙoƙarin gyara a riƙa duba irin yanayin da gidajen mu ke kasancewa na rashin kula da nuna ingantaccen tsarin tarbiyya bisa koyarwar addinin Musulunci. Haka anguwannin mu da makarantun mu, inda wasu daga cikin yaran matan da aka kama suke cewa sun baro gaban iyayensu ne don yin karatu a wata jiha, alhalin makarantun da suka ce suna yi basu da tsarin dakunan kwanan ɗalibai a cikin makaranta, shi ya sa suke kama ɗaki a cikin anguwanni.

Daga nan kuma wasu sai su shiga harkar bin maza da karuwanci, saboda su samu abin da za su riqe kansu, kuma su yi rayuwa irin ta sauran ɗalibai. Da yawa iyaye na tura yara irin waɗannan makarantu da ke wasu jihohi ba tare da sa ido kan irin rayuwar da suke yi ba, kuma ba tare da suna basu abin da zai riƙe su na game da abinci da kuɗin gudanar da karatu, yadda za su iya tsare mutuncinsu, ba tare da sun bi wasu maza ko ƙawayen banza ba.

Sannan mu sani akwai yaran da suke barin gaban iyayensu saboda yunwa da talauci, da zarmewar zuciya, ganin ba za su samu irin rayuwar da suke so a gida ba, sai su fake da zuwa wasu garuruwa ganin ’yan uwa alhalin ba can ɗin suke tsayawa ba, wajen wasu maza suke zuwa ko gidajen karuwai a inda suke ganin babu mai tsawatar musu. Babu mamaki lokacin da ’yan jarida ke hira da wasu daga cikin irin waɗannan ‘yan mata ke tambayarsu daga wacce jihar suka fito, domin tabbatar da ko su ’yan gari ne ko baƙi.

Karima (ba sunan asali ba ne) wata matashiyar budurwa ce da ke zaune tare da iyayenta a Jos, amma ganin ba ta samu miji ta yi aure a lokacin da iyayen ke ganin ya kamata ta bar gabansu, sai kawai ta nemi zuwa makarantar gaba da sakandire da garin Bauchi da ke maqwaftaka da Jos. A nan ne wannan matashiya ta kama ɗaki a wajen makaranta, ya zama mata kamar lasisin bin maza da sharholiya a maimakon karatun da ta ce wa iyayenta za ta yi. Sakamakon su ma iyayen ba su kula da sauke nauyinsu da ke kanta ba. Daga bin mazan da take yi ne take samun abin ɗaukar ɗawainiyar karatun da take yi.

Ita kuma Hauwa (ba asalin sunanta ba ne) ’yar asalin Jihar Katsina ce, da aka yi wa aure ba da mijin da take so ba. Don haka daga samun savani ta yi yaji zuwa gidan iyayenta, amma mahaifinta ya qi yarda ta zauna a gidan ya korata, daga nan sai ta wuce Kano wajen wata ƙanwar babarta da ke zaman kanta, inda ita ma ta samu wani gauro da ke nemanta suka koma zaman daduro da shi, a gidan da qƙanwar babarta zaune tana sheƙe tata ayar.

Waɗannan duka labaran mutane ne na gaske, da suka samu kansu cikin wata ƙazamar rayuwa, da ba ita suka zaɓawa kansu ba, sai ta dalilin rashin kyakkyawar tarbiyya da sakacin iyaye.

Saboda haka a daidai wannan gaɓar ina so in jawo hankalin hukumomi cewa ba kowanne lokaci ne za mu riƙa nisanta jihohin mu ko ’yan jiharmu da hannu cikin wannan baɗala ba, domin idan matan ba ’yan jihar ba ne, ai su masu neman su ’yan jihar ne. Don haka duk varnar ɗaya ce, kuma mataki ɗaya ya kamata a ɗauka. Batun cewa baƙi ne ke shigowa suna vata mana gari ba hujja ba ce, amma an binciki me yake jawo baƙin shigowa suna baza hajojinsu?

Lallai ina mai ba da shawara a duk lokacin da aka yi irin wannan kamen to, kafin a saki waɗanda aka kama su koma harkokin da, suka saba, gwamnati ta samar da wani tsari na riqe su, ko ɗaukar bayanansu in ma daga gidajen iyayensu za su riaa zuwa, a samar musu da sana’o’in dogaro da kai, da za su riqa yi don ɗauke hankalinsu daga fasadin da suke yi, a kuma haɗa su da wani jari na farawa. Kodayake, wasu da na saurari zantawar da aka yi da su suna cewa da sana’arsu, suna zuwa ne baza haja. Wani kuma da ya tabbatar da hakan ya ce, daga sayar da hajojin ne suke ɓigewa sayar da jikinsu ga mazan da, suka taya.

Kamar yadda Jihar Gombe ta ɗauki matakin rushe wasu gine-ginen da rijistar wasu wuraren, akwai buƙatar gwamnatin Jihar Kano ta rushe wasu gidajen da suka yi ƙaurin suna wajen zama matattarar ɓatagari, da baza jami’an tsaro don yin sintiri a sauran wuraren da ake kira gidajen gala ko kulob, don hana cigaba da bazuwar irin waɗannan ayyuka da ke ƙara haifar da rashin tarbiyya da tsaro.

A ƙarshe, ina kuma jan hankalin mahukunta lallai a shawo kan matsalar yunwa da tsadar rayuwa da ke damun al’umma. Idan talaka bai samu rufin asiri da abin da zai dogara da rayuwarsa ba to, fa tarbiyya za ta kuvuce a hannun iyaye, tsaro zai ƙara lalacewa, gwamnati za ta rasa ƙarfin faɗa a ji.