14
Dec
DAGA MUKHTAR YAKUBU An bayyana fitaccen malamin addinin Musluncin nan marigayi Sheikh Dakta Yusuf Ali wanda Allah ya yi wa rasuwa a farkon watan Nuwamban da ya gabata a matsayin wani managarcin malamin da ya yi shaharar da za a daɗe ba a manta da shi ba a fannin ilimi da kuma mu'amala da jama'a Wannan bayanin ya fito ne daga bakin shugaban majalisar malamai ta Arewa da kuma ta Jihar Kano Sheikh Ibrahim Khalil a lokacin da yake gabatar da jawabin sa a wani taro da gamayyar ƙungiyar marubutan Arewa da ƙungiyar ANA ta ƙasa reshen Jihar Kano suka shirya…
