Editor

9276 Posts
Farfesa a ABU ya maido Naira miliyan 1 da aka biya shi bisa kuskure

Farfesa a ABU ya maido Naira miliyan 1 da aka biya shi bisa kuskure

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban makarantar horas da sojoji NDA John-Ochefu Ochai a ranar Laraba ya ziyarci Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) dake Zariya domin ganawa da Farfesa Umar Ka’oje bayan ya maido da sama da Naira miliyan 1 da aka biya shi bisa kuskure. Kuɗaɗen da aka biya farfesan sun kai Naira miliyan 1,153,953.36. Waɗannan kuɗaɗen na aikin karantarwa da ya yi ne a NDA aka biya shi haƙƙinsa. Ochai ya zo Jami’ar tare da wasiƙa godiya da yabo daga NDA wacce ke ɗauke da kwanakin wata 12 ga Satumba, 2023. Shugabar sashen koyar da kwas ɗin ‘Political…
Read More
Matar gwamnan Kebbi za ta haɗa gwiwa da Intel Box don haɓɓaka ayyukan SDGs

Matar gwamnan Kebbi za ta haɗa gwiwa da Intel Box don haɓɓaka ayyukan SDGs

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi Matar gwamnan Kebbi Hajiya Zainab Nasir Idris nemi haɗin gwiwa tsakanin Nasara Foundation da Intel Box a kan muradun ƙarni SDGs. Ta yi wannan bayani ne a lokacin da ta kai ziyara a ofishin Intel Box Solution Ltd a Abuja babban Birnin tarayyar Nijeriya ranar Talatar da ta gabata. Ta ce wannan haɗin gwiwar zai yi tasiri wajen inganta rayuwar al'umma ta fannoni da yawa da suka haɗa da ilmin 'ya'ya mata, horas da makamai kiwon lafiya, mata masu ciki da jinjirai da kuma koyar da sana'o'in hannu ga mata da matasa. Ta ƙara…
Read More
Ba mu bayar da umarnin janye tsofaffin takardun kuɗin Naira ba – CBN

Ba mu bayar da umarnin janye tsofaffin takardun kuɗin Naira ba – CBN

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya ce duk takardun kuɗi (tsofaffi da sababbi) suna nan a kan doka. Wannan na zuwa ne sakamakon fargabar da ake ciki cewa tsofaffin takardun kuɗi za su daina aiki nan da watan Disamba 2023. Wata sanarwar da mai magana da yawun bankin CBN, Isah Abdulmunin ya fitar a ranar Laraba, ta ce bankin bai bayar da umarnin janye tsofaffin takardun kuɗi ba daga wajen al'umma. Bankin ya ce, “An kuma samu rahotannin damuwa da wasu jama’a ke nunawa kan halacci ko rashinsa na tsoffin takardun kuɗin Naira. “Don kauce wa shakku,…
Read More
An bindige mai kaɗa ƙuri’a har lahira a rumfar zaɓe a Kogi

An bindige mai kaɗa ƙuri’a har lahira a rumfar zaɓe a Kogi

Daga BASHIR ISAH Rahotanni daga Jihar Kogi sun ce wani mai suna Umar Hassan ya rasa ransa bayan da aka harbe shi da bindiga a wajen zaɓen gwamna da ke gudana a jihar. MANHAJA ta kalato cewa, hakan ya auku ne ranar Asabar a rumfar zaɓe ta Agala Ogane a yankin Anyigba da ke Mazaɓar Sanatan Kogi ta Gabas. Sai dai ya zuwa haɗa wannan labari, babu bayani a hukumance daga ɓangaren hukumomin tsaro kan batun. Wata majiya ta ce wasu da ake zargin 'yan barandan siyasa ne suka yi kisan. Mai magana da yawun Jam'iyyar APC na kwamitin yaƙin…
Read More
Sarkin Bauchi ya buƙaci ‘yan kasuwa su rage farashin kayayyakin masarufi

Sarkin Bauchi ya buƙaci ‘yan kasuwa su rage farashin kayayyakin masarufi

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi Mai Martaba Sarkin Bauchi, Dokta Rilwanu Suleiman Adamu a cikin makon da ya gabata ya kai ziyarar bazata ga wasu kasuwanni dake cikin birnin Bauchi da kewayenta domin ganewa kansa yadda 'yan kasuwa suke zuga farashin kayayyakin masarufi da zumar yi masu nasihar ta natsu. Yayin ziyarar ta bazata, Mai Martaba Sarkin ya kekkewaya kasuwanni da suka haɗa da wacce take Wuni, Muda Lawal da kuma ta Wajen Durum dake wajen gari, inda yayi hulɗoɗi da 'yan kasuwa domin ya jiyewa kansa ire-iren farashin kayayyakin masarufi, husasan ma masara, dawa, gero, alkama, da dai sauran…
Read More
Haƙƙi na ne fitar da Arsenal kunya – Arteta

Haƙƙi na ne fitar da Arsenal kunya – Arteta

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kocin Arsenal, Mikel Arteta ya bayyana cewa, dole ne ya fitar da ƙungiyar kunya a idon duniya bayan wasar da suka lallasa Sevilla da ci 2-0 a gasar Zakatun Turai. A kwanakin baya ma ya ce, ya zama wajibi ya kare kulob ɗin bayan ya caccaki alkalin wasa a karawar da Newcastle ta doke su da ci 1-0 a ranar Asabar ɗin da ta gabata. Ya ce, shawarar da aka yanke kan ƙwallon Anthony Gordon a St James' Park "abin kunya ne" kuma "abin takaici". Arsenal ta goyi bayan kalaman Arteta a wata sanarwa da ƙungiyar…
Read More
Pepe ya kafa sabon tarihi a gasar Zakarun Turai

Pepe ya kafa sabon tarihi a gasar Zakarun Turai

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ɗan wasan baya na Portugal Pepe ya zama ɗan wasa mafi yawan shekaru da ya zura ƙwallo a raga a tarihin gasar zakarun Turai, inda ya ci qwallon da ta taimaka wa FC Porto ta doke Royal Antwerp. Pepe mai shekaru 40 da kwana 254 da haihuwa, ya zura ƙwallo ta biyu a ragar Antwerp a minti na 91, inda ya zama ɗan wasa na farko da ya haura 40 da ya zura ƙwallo a gasar. Francesco Totti ke riƙe da tarihin mai mafi yawan shekaru da ya zura ƙwalo a shekara 38 da kwanaki 59.…
Read More
An horar da ƙananan ‘yan kasuwa 102 dabarun inganta sana’o’i na zamani

An horar da ƙananan ‘yan kasuwa 102 dabarun inganta sana’o’i na zamani

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano Ƙwararru kan harkokin kasuwancin da suka fito daga ɓangarori daban-daban sun shawarci ƴan kasuwa da masu ƙananan masana'antu su rungumi sabbin hanyoyin kasuwanci da fasahar sadarwa ta zamani, domin bunƙasa sana'o'insu. An yi wannan kiran ne a wajen taron da Dandalin Horarwa Kan Dabarun Sana'o'in Zamani na Mu Inganta Sana'armu wanda ya gudana a birnin Kano, da nufin wayar da kan ƙananan ƴan kasuwa, da samar da muhallin da za su baje-kolin sana'o'insu, don sabbin abokan hulɗa da ƙulla ƙawance tsakanin ƴan kasuwa da masu masana'antu. Taron Mu Inganta Sana'armu wanda shi ne irinsa na…
Read More
Har ƙasar Saudiyya muna aikin ciyar da abinci – Hajiya Hannatu

Har ƙasar Saudiyya muna aikin ciyar da abinci – Hajiya Hannatu

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano Hajiya Hannatu Tijjani Haruna Shugabar gidan abinci na 7:30 dake Kano, ta bayyana cewa daga kafuwar wannan gida ta horas da dubban mata sana’o'i da irin wannan aiki na gidan abinci kyauta da kuma samar wa mutane musamman matasa maza da mata sama da 3,000 domin su dogara da kansu. Hajiya Hannatu ta ce yanzu haka tana tare da wasu, inda wasu kuma suka buɗe nasu don tsayawa da ƙafafuwansu sakamakon horon da suka samu a Kiminu Food. "Don haka ina farin ciki da samun wannan dama daga Ubangiji," inji ta. Hajiya Hannatu Tijjani Haruna…
Read More
Gwamna Dauda Lawal ya ƙuduri aniyar kafa rundunar ‘yan bijilanti a Zamfara

Gwamna Dauda Lawal ya ƙuduri aniyar kafa rundunar ‘yan bijilanti a Zamfara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamnatin Jihar Zamfara ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal ta bayyana cewa ta tayar da azama wajen yaƙi da 'yan bindiga da sauran miyagun ayyuka a duk faɗin jihar, inda ta ce za ta samar da runduna ta musamman don tabbatar da tsaro a duk faɗin jihar.  Gwamna Lawal ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin da ya ke bayani game shirin da gwamnatin ta yi na zaƙulo wasu matasa daga Ƙananan Hukumomin jihar 14, waɗanda za su yi aikin samar da tsaro a Hukumar tsaron da gwamnatin za ta kafa mai suna 'Community Protection Guards (CPG),…
Read More